150513-An-kawar-da-Ebola-a-Liberia-Sanusi.m4a
|
A farko watan Maris na shekarar 2014 ne aka fara gano wasu mutane da suka kamu da cutar ta Ebola a yankin Lofa da ke kasar Liberia. Kana a watan Yuli annobar ta barke a kasar baya da aka kwantar da wani mutum a wani asibitin kasar da ke dauke da cutar daga kasar Saliyo.
Shugabar kasar Liberia, Madam Ellen Johnson Sirleaf ta ce, baki dayan Liberia na farin ciki da wannan nasara, Sai dai ta ce za a dauki tsawon lokaci kafin a manta da wannan al'amari. Tuni kuma 'yan kasar suka koma gudanar da harkokinsu na yau da kullum
Kungiyoyin agaji da hukumomin kasa da kasa da gwamnatocin kasashen duniya daban-daban ciki har da kasar Sin sun taimakawa kasar ta Liberia da magunguna, likitoci, kayayyakin kiwon lafiya da shawarwari wajen ganin ta kubuta daga wannan annoba.
Bayanai na nuna cewa, cutar Ebola ta yi mummunan illa ga fannonin kasar daban-daban kamar ilimi, tattalin arziki, kiwon lafiya da dai sauransu. Alkaluma na kuma nuna cewa, mutane sama da dubu 4 ne cutar ta halaka a kasar Liberia.
Masana na cewa, duniya ta koyi darasi daga cutar kuma lokaci ya yi da za a kara yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a fannonin musayar bayanai na kiwon lafiya da dabarun kare yaduwar cututtuka don tinkarar duk wata annobar da ta kunno kai don gudun salwatar rayukan bayin allah kamar yadda cutar Ebola ta haddasa a sassa daban-daban na duniya, musamman kasashen da ke yammacin Afirka. (Ibrahim/Sanusi Chen)