Mamban jam'iyyar NCP, Kamal Omer ya ce, NCP ta sake yin alkawarin yunkurin shawarwari, don aiwatar da yarjejeniyar da aka daddale tsakaninsu. Ganawa da bangaren 'yan adawa a kasar daban ya nuna cewa, gwamnatin ta sassauta kuma tana da sahihiyar zuciya, don haka ya kamata 'yan adawa su yi amfani da wannan dama don shiga cikin yunkurin siyasa. Omer ya kuma jaddada cewa, ba ya fata kasashen waje sun yi shisshigi game da yunkurin shawarwarin ba.
Jam'iyyar adawa RNM tana ganin cewa, yarjejeniyar Addis Ababa da aka daddale tsakanin gwamnatin Sudan da 'yan adawa, za ta kawo sabon kuzari game da shawarwari tsakaninsu.(Bako)