An ce, a filayen gonaki na Bafata, da Kabu dake gabashin kasar Guinea-Bissau, kwararrun ilmin gona na kasar Sin dake kasar sun fito da wani nau'in irin shinkafa mai suna "Sabe12" ga manoman wurin da ba su da tsarin ban ruwa. Shinkafar kuwa ta samu karbuwa sosai daga wajen manoman sakamakon kamshinta da dandanonta da aukinta.
Kaza lika yabanyar da suka samu bayan gwada wannan nau'in irin shinkafa ya ninki sau da dama, idan aka kwatanta da irin "Banimalo", wanda manoman suke amfani da shi a da.
Bisa kiyasi, a lokacin rani yawan karuwar amfanin da manoman suka samu ya kai sama da rubi 3, yayin da a lokacin damuna wannan adadi ya karu da kashi 26 cikin 100. (Bako)