in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya yi kakkausar suka game da harin da aka kai wa sojojin kiyaye zaman lafiya a Kongo(kinshasa)
2015-05-06 16:23:47 cri
Babban magatakardan M.D.D. Ban Ki-Moon ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa sojojin kiyaye zaman lafiya na M.D.D. da ke yankin gabashin kasar Kongo(kinshasa).

Ban Ki-Moon ya fadi hakan ne a jiya Talata ta bakin kakakinsa. Rahotanni na cewa, harin da aka kai ya yi sanadiyar mutuwar sojojin kiyaye zaman lafiya, 'yan kasar Tanzaniya guda 2 tare da jikkatar wasu 13, baya ga wasu 4 da suka bace. An kuma kai harin ne, lokacin da kungiyar kiyaye zaman lafiya ta M.D.D. dake kasar Kongo(kinshasa) ke gudanar da ayyukan kiyaye fararen hula.

Sanarwar ta ce, Ban Ki-Moon ya yi kakkausar suka game da wannan aika-aika.Yana mai cewa, M.D.D. za ta ci gaba da dukufa ka'in da na'in wajen daukar hakikanan matakan da suka dace da kudurorin kwamitin sulhu na M.D.D., don kiyaye lafiyar fararen hula da dakile masu dauke da makamai da ke yankin gabashin kasar Kongo(kinshasa).(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China