in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mashawarcin shugaban Nijeriya ya ce, kasar Sin ta canja a yau da kullum
2015-04-28 12:56:50 cri


Kwanan baya, yayin da mai ba da shawara ga shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan, kuma tsohon mukaddashin shugaban 'yan jaridun Nijeriya, kuma tsohon mataimakin shugaban kungiyar 'yan jaridun yammacin Afrika Nasiru Zaharadeen ke zantawa da mu, ya bayyana cewa, kasar Sin babbar kasa ce da ta yi fici a duniya wajen habakar tattalin arziki, ya zo kasar Sin domin halartar Canton Fair da aka shirya a birnin Guangzhou na kasar Sin.

Kasar Sin da ta gani a yanzu, ta sha bamban da yadda ta gani a cikin shekaru da dama da suka gabata, yayin da a shekaru da dama da suka wuce, yayin da yake rike mukamin mukaddashin shugaban 'yan jaridun Nijeriya, ya taba zuwa kasar Sin, har ma ya gana da shugaban kasar Sin Deng Xiaoping a wannan lokaci, kuma yana ganin cewa, hangen nesa da shugaba Deng Xiaoping yake da shi yana da amfani har yanzu, musamman ma manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje da ya gabatar. Yana mai cewa, a lokacin zuwansa, babban filin jiragen sama na Beijing bai kai na birnin Kano ba. Haka kuma, jirgin kasa daga Guangzhou zuwa birnin Shanghai ya kan shafe awoyi 24, yanzu, ko jirgi na marasa sauri bai shafe awoyi 6 ba. Yana fatan Nijeriya za ta ci gaba da koyo daga kasar Sin.

Yayin da aka tabo maganar manufar diplomasiyya da ke tsakanin Nijeriya da Sin, yana ganin cewa, Gen. Muhammadu Buhari zai ci gaba da wannan kyakkyawar alaka da ke tsakaninta da Sin, sabo da bisa Alkur'ani mai tsarki, duk wanda yake so neman ilmi, kome nisa, har ma kasar Sin, ya kamata shi yake zuwa. Haka kuma, ya yi imani cewa, a karkashin mulki na shugaban Buhari, za a nuna darajar Nijeriya daga  duk wani bangare.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China