Bisa kididdigar da aka samu, an ce, yawan Musulmai a duniya zai karu zuwa biliyan 2.8 a shekarar 2050, yayin da wannan adadi ya kai biliyan 1.6 a shekarar 2010. Ya zuwa wancan lokaci, yawan Musulmai zai kai kashi 1 cikin 3 na yawan al'ummar duniya.
Kididdigar ta kuma nuna cewa, yanzu, kashi 1 cikin 3 na Musulmai a duniya suna zama a yankin Gabas ta Tsakiya da nahiyar Afrika, kuma wadannan yankunan ne da ake samun karuwar yawan al'umma mafiya yawa, kuma yankuna ne da ake samun karuwar Musulmai mafi yawa a duniya.(Bako)