in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya bayyana damuwa game da fasa kwaurin 'yan ci rani ta tekun Mediterranean
2015-04-22 09:57:40 cri

Kwamitin tsaron MDD ya bayyana matukar damuwa, game da yadda wasu bata-gari ke ci gaba da fasa kwaurin baki 'yan ci rani ta tekun Mediterranean zuwa kasashen Turai.

Cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar a jiya Talata, ya ce, a baya-bayan nan ana samun karin masu jefa rayukan 'yan ci ranin cikin mummnan hadari ta hanyar jigilar su ta teku.

Sanarwar ta bayyana wannan lamari da cewa laifi ne babba, wanda ke barazana ga yankin Turai, don haka ya zama wajibi a dauki matakan hukunta masu aikata shi.

Rahotanni na cewa, a ranar Lahadin da ta gabata, kimanin 'yan ci rani 800 ne ake zaton sun rasa rayukansu, yayin da jirgin da ke dauke da su ya nutse, a wani wuri kusa da tsibirin Sicily na kasar Italiya.

Don gane da hakan ne kuma kwamitin tsaron MDDr ya bukaci daukacin kasashen da wannan lamari ya shafa, da su hada kai da hukumomin kasa da kasa, da na shiyya-shiyya, ciki hadda hukuma mai kula da harkokin 'yan ci rani ta duniya IOM, wajen dakile kwararar bakin haure, tare da kawo karshen kazamar sana'ar fasa kwaurin bil'Adama a yankin. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China