in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron manyan jami'ai na kasashen Asiya da Afrika a Indonesiya
2015-04-19 17:47:48 cri

An bude taron manyan jami'ai na kasashen Asiya da Afrika mai jigon "Kara hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa da wanzar da zaman lafiya a duniya", wanda ke da zummar tunawa da cika shekaru 60 da kiran taron Asiya da Afrika, a yau Lahadi ran 19 ga wata a birnin Jakarta na kasar Indonesiya.

Manyan jami'ai na kasashen Asiya da Afrika 88 da suka hada mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin Liu Zhenmi sun halarci taron. .

Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Indonesiya ta nuna cewa, wakilan kasashe 88 da shugabannin kasashe 34 sun tabbata zasu halarci taron murnar cika shekaru 60 da kiran taron Asiya da Afrika daga ran 19 zuwa 24 a Jakarta da Bandung. Taron kuma zai tattauna kan manyan batutuwa 3, ciki hadda marawa Palasdinu baya, kara hadin gwiwa da sada zumunci tsakanin kasashen Asiya da na Afrika bisa sabbin tsare-tsare da sake nanata tunanin taron Bandung da sauransu.

Kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Indonesiya Arrmanatha Nasir ya nuna cewa, wakilan kasa da kasa da za su halarci bikin tunawan sun kai 1800, yawan 'yan jarida da suka yi rajistar zuwa ya kai 1300, ban da haka kuma, 'yan kasuwa 480 za su halarci taron kolin cinikayya tsakanin Asiya da Afrika, an kiyasata cewa,yawan mutane da za su halarci taron zai kai 3600 ko fiye.

Indonesiya za ta tura sojojinta 26,000 da 'yan sanda 9,700 don samar da tsaro ga bikin. Dadin dadawa, kasar ta girka jiragen sama da na ruwan yaki don tabbatar da lafiyar shugabannin kasa da kasa.

An ba da labari cewa, da wannan taron manyan jami'ai ne aka fara bukukuwan murnar cika shekaru 60 da taron Asiya da Afirka, kuma za a kira taron ministoci a ran 20 ga wata, yayin da kuma za a kira taron kolin cinikayya tsakanin Asiya da Afrika a ran 21 ga wata, dadin dadawa, wakilan kasashen Asiya da Afrika za su yi tafiya daga Otel din Savoy-Homan a Bandung su ratsa babban ginin taron Asiya da Afrika har zuwa filin tsakiya na birnin a ran 24 ga wata, hanyar da ta sheda tarihin taron Asiya da Afrika da aka kira a shekarar 1955. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China