150401-Shirin-Amurka-na-sake-tattaunawa-da-shugaba-Asad-na-Sham-Sanusi.m4a
|
John Kerry ya ce,tattaunawar Geneva da aka yi har sau biyu a watan Yunin shekara ta 2012 da kuma watan Janairun shekara ta 2014 duk ba su kai ga kawo karshen rikicin kasar ta Sham ba, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 220,000 kana fiye da rabin mazauna kasar aka tilasta musu tsere wa daga gidajensu,yayin da kusan mutane miliyan 4 ke gudun hijira a sansanonin 'yan gudun hijira dake kasashe makwabta.
Shirin gwamnatin Obama game da Sham yana zuwa ne sakamakon karin sukar da ya yake sha a gida da waje, ganin yadda a baya ya nace cewa, saukar da shugaba Assad daga mulki ne kadai mafita kan sulhunta batun kasar Sham, sai kuma yanzu ya yi shiru tun bayan da kasar ta kai hari a kan 'yan kungiyar IS a kasashen Iraqi da Sham a shekarar bara.
Masu sharhi na dora laifin rashin mutunta yarjejeniyar kan shugaban kasar ta Sham Bashar al-Assad wanda ya sa dukkan wadannan yarjejeniyoyi wargaje wa.Yanzu haka Amurka na kokari tare da sauran masu ruwa da tsaki don ganin an sake cimma wata mafita ta diflomasiyya, maimakon amfani da karfin soja.(Ibrahim/Sanusi Chen)