150318-Yadda-Sin-ke-zurfafa-yin-gyare-gyare-a-gida-zai-ba-ta-damar-cimma-burinta-Sanusi.m4a
|
Sharhin ya ce, kafa zamantakewar al'ummar kasa a dukkan fannoni na da ma'ana a fannoni guda hudu, na farko wannan aiki zai shafi dukkan jama'ar kasar Sin, da kuma dukkanin sassan kasar, na biyu za a tafiyar da ikon mulkin kasar ba tare da cin hanci da rashawa ba, na uku za a inganta karfin kasar, da kyautata zaman rayuwar jama'ar ta, na hudu za a tabbatar da adalci a shari'a da dokoki a kasar.
A yayin da ake kokarin raya kasa daga fannoni hudu; wato kafa zamantakewar al'umma mai annashuwa da jituwa, da zurfafa yin kwaskwarima, da gudanar da harkokin kasa bisa dokoki, da daukar kyawawan matakan gudanar da harkokin jam'iyyar kwaminis ta kasar, kafa zamantakewar al'umma mai annashuwa da jituwa shi ne buri na farko da ake fatan cimma nasarar sa.
Masu fashin baki na ganin cewa, amfani da aikin zurfafa yin kwaskwarima wajen warware manyan matsaloli yayin da ake raya kasar ta Sin, da tabbatar da zamanintar da kasar ta hanyar gudanar da harkokin kasar bisa dokoki kana da daukar tsauraran matakai wajen gudanar da harkokin jam'iyya don zurfafa tushen gudanar da harkokin kasar, matakai ne da za su taimaka wajen kammala kafa zamantakewar al'umma mai annashuwa da jituwa yadda ya kamata.
Idan kuma hakan ya gudana kamar yadda aka tsara tabbas ne zurfafa yin gyare-gyare da kasar Sin ke yi a dukkan fannoni zai habaka tsarin gurguzu mai halin musamman na kasar Sin, kuma zai samar wa kasar wani karfin cimma burinta. (Ibrahim/Sanusi Chen)