in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanin kasar Sin kan harkokin Afirka ya jinjina babban zaben da aka yi a kasar Najeriya
2015-04-01 16:25:30 cri

Babban zaben da aka yi a kasar Najeriya ya jawo hankalin jama'ar kasar Sin sosai, inda masanan kasar masu binciken harkokin kasashen Afirka suka jinjina zaben.

Da safiyar Laraban bisa agogon kasar Sin, aka sanar da sakamakon babban zaben kasar Najeriya na shekarar 2015, kan cewar tsohon shugaban mulkin sojin , Janar Muhammadu Buhari na jam'iyyar adawa ta APC ya lashe zaben. Game da batun, wakiliyarmu ta zanta da Farfesa Liu Hongwu, mataimakin shugaban kungiyar nazarin harkokin Afirka ta kasar Sin, inda ya yaba akan yadda aka yi zaben da kuma bayar da sakamakonsa. Tun da wannan ne karon farko a tarihin demokuradiyyar Najeriya da aka doke shugaban da yake kan karagar mulki tun bayan samun 'yancin kan kasar a shekarar 1960 daga turawan Ingila, Farfesa Liu ya ce, wannan ya sheda ci gaban yunkurin demokuradiyyar Najeriya.

"Wannan ne karo na farko da jam'iyyar adawa ta lashe zabe a cikin takarar da ke tsakaninta da jam'iyyar da ke kan karagar mulkin kasar, musamman ma a wannan lokacin da ake ganin saurin ci gaban tattalin arzikin kasar da kuma kyautatuwar zaman rayuwar jama'a bayan shekarar 1999 da jam'iyyar PDP ta shugabanci kasar. Cimma nasarar aikin musayar ikon mulkin kasa a Najeriya ya sheda kyakkyawan tsarin siyasa na kasar da kuma ci gaban yunkurin demokudiyyarta."

A bana, ban da Najeriya, akwai sauran kasashen Afirka da dama da za su gudanar da babban zabe, ciki har da Nijar, Togo, Sudan ta Kudu, Mali, Burundi da dai sauransu. Farfesa Liu Hongwu ya furta cewa, a matsayinta na wata muhimmiyar kasa a Nahiyar Afirka, gudanar da babban zabe cikin adalci da lumana a kasar Najeriya ya zama abin koyi ga sauran kasashen Afirka. Ya ce,

"A da, tashe-tashen hankali ya kan faru a ko wane zabe na kasashen Afirka, amma wannan hali ya kyautatu a yawancin kasashen Afirka a 'yan shekarun nan. Najeriya kuwa ita ja-gora a Afirka, bayan abkuwar tashe-tashen hankali sau da dama, yanzu ta riga ta samu wani tsarin musayar ikon mulkin kasa mai dacewa. Don haka ina ganin cewa, gudanar da babban zabe a Najeriya lami lafiya zai yi babban tasiri ga kokarin samun kwanciyar hankali a sauran kasashen Afirka."

Yaya dangantakar da ke tsakanin Sin da sabuwar gwamnatin kasar Najeriya a nan gaba? ko Janar Buhari zai canja manufofin kasarsa kan kasar Sin? Game da batun, Farfesa Liu yana sa ran ganin ci gaban dangantakar kud-ta-kud a tsakanin bangarorin biyu nan gaba. Ya kara da cewa,

"Dangantaka a tsakanin kasashen Sin da Najeriya ta samu saurin bunkasuwa tun bayan shekaru 90 na karnin da ya gabata. Yanzu kasar Sin muhimmiyar abokiya ce ta Najeriya a fannin zuba jari da cinikayya. Yanzu hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu na da matukar muhimmanci gare ta. A shekarun nan, a kan gudanar da ayyukan hadin kansu a kudancin kasar Najeriya. Amma sabo da Janar Buhari ya zo daga arewacin kasar, don haka ina ganin cewa, mai yiwuwa yawan ayyukan hadin gwiwar kasashen biyu da za a gudanar a arewacin kasar nan gaba zai karu."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China