150330-ministan-hanyoyin-ghana-ya-ce-bako.m4a
|
Kwanan baya, yayin da ministan dake kula da harkokin hanyoyi na jamhuriyar Ghana Alhaji A.B. Inusah Fuseini ke zantawa da wakilinmu, ya bayyana cewa, kasar Ghana tana maraba da masu saka jari na Sin da za su je kasar Ghana don gina manyan ababen more rayuwa a kasar, kuma Ghana za ta kokarta don taimaka musu idan za su bi dokokin kasar. Ya ce, a 'yan shekarun nan da muke ciki, Ghana ta samu matsaloli da dama dake shafar hanyoyi, yana fatan Sinawa za su tashi tsaye don taimakawa kasar. Sabo da ya taba jin karin maganar basine wai "Idan aka so samun ci gaba, dole ne a gina hanyoyi a farko."Yana sa ran ci gaba da hadin gwiwa da kasar Sin, don samun kwalliya biya kudin sabulu wajen raya hanyoyin kasar.(Bako)