Kaza lika, daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2014, matsakaicin saurin bunkasuwar da sha'anin aikawa da kaya cikin sauri ya samu, ya kai kashi 50.3 cikin 100, adadin da ya ninka har sau 6 bisa na saurin karuwar GDP a daidai lokacin.
A 'yan shekarun nan, sha'anin aikawa da kaya cikin sauri na Sin ya samu habaka cikin hanzari, kuma hidimomin da aka bayar sun samu ingantuwa sosai, kana an kara yalwata hidimomin, don kara kawo sauki ga jama'a a wannan fanni.(Bako)