150304-Ziyarar-da-gwamnan-jihar-a-Najeriya-ya-kawo-nan-CRI-Sanusi.m4a
|
Gwamna Kwankwaso ya bayyana cewa, baya ga sauran kasashen duniya kamar Malaysia, Masar, Poland, Ukraine, Indiya, Ingila da Amurka, akwai kuma kimanin dalibai 25 'yan asalin jihar Kano da ke karatun digiri na biyu da na uku a sassa daban-daban na kasar Sin galibinsu 'ya'yan talakawa.
Yanzu haka, akwai daliban jihar ta Kano sama da dubu biyu da ke karatu a sassa daban-daban na duniya, baya ga wadanda ke karatu a jami'o'i, da sauran manyan makarantun Najeriya.
Injiniya Kwankwaso ya ce, gwamnatin jihar Kano ta gina dakunan kwanan dalibai a jami'o'i daban-daban a tarayyar Najeriya ta yadda wadannan jami'o'i za su rika daukar daliban jihar.
Gwamnan na Kano ya kuma ce, yanzu haka akwai kamfanonin kasar Sin da ke gudanar da ayyukan samar da kayayyakin more rayuwa a jihar kamar gadoji da hanyoyi da ayyukan samar da ruwa da ilimi da sauransu sannan ya tabo kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka.
Bugu da kari, ya yi magana a kan siyasar Najeriya da yadda gwamnatinsa ke samar da muhimman kayayyakin more rayuwa da sauran ayyukan da inganta rayuwar al'ummar jihar kano baki daya. (Ibrahim/Sanusi Chen)