in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin kasar Sin ta gabatar da manufofinta na shekarar 2015
2015-03-05 16:46:39 cri

A safiyar Alhamis din nan ne wakilan majalisar jama'ar kasar Sin su kimanin 3000, suke gudanar da taro a dakin taron jama'ar kasar Sin, domin aiwatar da ikonsu na wakilcin dukkanin Sinawa.

Ana sa ran wakilan za su nazarci rahoton gwamnatin kasar, tare da kada kuri'u kan shi, matakin da zai kai ga yanke shawara kan manufofin da Sin za ta dauka a wannan shekarar da muke ciki.

Rahotanni na cewa a halin yanzu, kasar ta Sin na fuskantar kalubalen tafiyar wahainiya a fannin ci gaban tattalin arziki, inda a shekarar da ta gabata, jimilar GDPn kasar dake bayyana halin tattalin arzikin kasar, ta kai kashi 7.4 bisa dari, matsayi da ya zamo mafi karanta a cikin shekaru 24 da suka gabata. Duk da haka, wannan jimilla tana sahun gaba a duniya ta fuskar tattalin arziki, kuma a daya hannun gwamnatin kasar ta Sin na fuskantar matsin lamba sosai. Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya ce,

"Halin da ake ciki ya kara matsi bisa na bara. Ana karancin samun jari, kuma babu bukatu a cikin gida sosai, kuma ba a samun ci gaba sosai a kasuwannin duniya, ga shi kuma ana fuskantar mawuyacin hali wajen samun bunkasuwar tattalin arziki mai karko, baya ga gamuwa da ake yi da wasu kalubaloli a wasu sana'o'i."

Game da hasashen da ake yi kan jimillar GDP a shekarar 2015, Mr Li ya ce,

"Burinmu na samun bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a wannan shekarar da muke ciki shi ne, samun GDP na kashi 7 bisa dari. Farashin kayayyakin yau da kullum ya karu da kashi 3 bisa dari, kuma a kara samar da guraben aikin yi a birane da garuruwa fiye da miliyan 10."

Mr Li ya yi bayani na musamman cewa, an fitar da wannan jimilla ta samun karuwar saurin bunkasuwar tattalin arziki na kashi 7 cikin dari, bisa bukatun mutane da yiwuwar cimma hakan, wanda hakan zai dace da bunkasuwar tattalin arziki, da kwaskwarima da za a yi a wannan fanni. Mr. Li ya kara da cewa,

"Za a tabbatar da hasashen kayayyaki dake dacewa da zamani idan an nacewa burin samun saurin bunkasuwar tattalin arziki a halin da ake ciki. An samar da tabbaci ga bunkasuwar tattalin arziki, da zummar samar da isassun guraben ayyukan yi, da samun saurin bunkasuwar tattalin arziki na kashi 7 bisa dari, wanda zai ba da tabbaci ga samar da isassun guraben aikin yi, saboda ganin bunkasuwar sha'anin ba da hidima da karuwar kananan kamfanoni da GDP. Ya kamata, wurare daban-daban sun yi iyakacin kokari bisa karfinsu don samun ci gaba mai nagarta."

Dadin dadawa, Mr. Li ya gabatar da tsarin da Sin za ta dauka, wanda zai dace da hali mai dorewa, dake bambanta da hali da aka fuskanta a baya, a fannin kara yin kwaskwarima da yin aikin kirkire-kirkire. Ya ce,

"Mai da hankali sosai kan aikin yin kwaskwarima, da zura ido kan muradunmu biyu, wato na samun bunkasuwar tattalin arziki bisa matsakaicin sauri a matsakaicin matsayi, wanda zai shige sahun gaba a duniya, da kuma hada tsarin ba da tabbaci ga manufofi, da hasashen da muke yi, da sa kaimi ga aikin yin kwaskwarima tare, sannan kuma da ciyar da tsarin yin kirkire-kirkire da samar da karin kayayyaki, da hidima ga jama'a gaba, daga baya kuma mu tabbatar da samun bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin mai inganci."

Wannan shekara ta kasance shekara ta biyu da ake zurfafa yin kwaskwarima. Game da kalubalolin da ake fuskanta wajen sauyin hanyar da za a bi a wannan fanni, yin kwaskwarima ya kasance babban matakin da gwamnatin ke dauka wajen daidaita halin da ake ciki. Rahoton gwamnatin da aka fitar a Alhamis din nan yana da ma'ana kwarai, Mr Li ya yi bayani cewa,

"Bai kamata, gwamnati ta aiwatar da ikonta yadda take son ba. Ya dace a saukakken ikonta, a rarrage ayyukanta, ta wannan hanya ne za a inganta karfin kasuwa."

Shekaru biyu bayan sabbin shugabannin kasar Sin sun ja karagar mulki, an tsige manyan shugabanni fiye da 80, bisa laifuka masu alaka da cin hanci da karbar rashawa. Game da wannan batu, Mr Li ya ce,

"Ya kamata mu mai da hankali sosai ga sa ido kan ayyukan manyan shugabanninmu a fannoni daban-daban, ciki hadda harkar kudade, da albarkatun kasa da kuma kadarorin kasa. Ban da haka, kamata ya yi a dauki tsauraran matakan yaki da cin hanci da karbar rashawa, ba kuma za a kau da ido kan irin wadannan laifuka ba ko kadan."

A cikin kwanaki 10 masu zuwa, wakilai fiye da 3000 za su aiwatar da ikonsu, na bincike da dudduba rahoton gwamnati, wanda za a kada kuri'u kan abubuwan da suka kunsa a ranar da za a rufe taron. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China