in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sassan daban daban na kasar Sin suna fatan ganin alfanun kwaskwarima a yayin taron NPC da CPPCC da za a gudanar
2015-03-02 16:36:58 cri

Za a kaddamar da taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar CPPCC a wannan mako a birnin Beijing, inda za a samu halartar wakilan majalisun biyu daga dukkan fadin kasar, domin ba da shawarwarinsu kan yadda za a karfafa aikin yin kwaskwarima a kasar a wannan shekarar da muke ciki. A gabannin wadannan taruka biyu kuwa, mutane daga sassa daban daban na fatan ganin alfanun kwaskwarima da suka shafi manufofin kasa da zaman rayuwar jama'a a yayin tarukan.

A kan dauki tarukan NPC da CPPCC da a kan yi a ko wace shekara a matsayin muhimmin dandalin da ake samun zarafin tsara manyan manufofin kasar Sin domin kara martaba ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma. Don haka a kan dora muhimmanci matuka kan muhimman batutuwan da za a tattauna a yayin tarukan biyu, ciki har da tattalin arziki, yaki da cin hanci da rashawa, yin kwaskwarima, da dai sauransu.

A fannin tattalin arziki, mai yiyuwa ne za a fi son ambatar jimlar "sabon tsarin yau da kullum kan tattalin arzikin kasar Sin" a yayin tarukan biyu. Ana fatan za a iya ba da amsa kan tambayoyin da suka shafi yadda za a tantance halin tattalin arziki da kasar Sin ke ciki, yadda za a iya gudanar da harkokin tattalin arziki yadda ya kamata, gami da yadda za a tabbatar da hasashen karuwar GDP. Game da wannan, kwararru a fannin tattalin arziki su ma sun yi bayani bisa saninsu. Shao Yu, babban kwararre a fannin tattalin arziki na kamfanin hada-hadar hannayen jari na Orient Securities na kasar Sin ya bayyana cewa,

"An kiyasta cewa, karuwar jimillar GDP za ta kai kashi 7 cikin kashi dari a shekarar 2015. A galibi dai, akwai gibi a tsakanin dunkulewar kasashen duniya, da karuwar tattalin arziki ta tsahon yayi, kana da aikin kwaskarima. Idan ba a iya haye wadannan wahalhalu ta hanyar tsara manufofi ba a wannan shekara, to za a kara hadarin tattalin arziki."

Batun yaki da cin hanci da rashawa shi ma ya jawo hankalin mutane sosai. Kafin bude tarukan biyu, an yanke hukunci kan manyan kusoshi fiye da goma da ake tuhuma da aikata da laifin cin hanci, wannan na nuna cewa babu shakka za a ci gaba da tattaunawa kan batun yaki da cin hanci da rashawa a yayin tarukan. Game da wannan, Yang Zhao, wakilin gidan talibijin na EASTERN na yankin Taiwan na kasar Sin ya ce,

"A shekaru biyu da suka gabata, an kara karfi kan yaki da masu cin hanci da rashawa, lamarin da ya jawo hankalin 'yan kallo na yankin Taiwan sosai, musamman ma kan lamuran kama da gurfanar da wasu manyan kusoshi da suka aikata da laifin."

A cikin batutuwan da za a tattauna a kai kan ci gaban kasar Sin, an fi mai da hankali kan batun yin kwaskwarima da na gudanar da harkokin kasa bisa doka. Shekarar bana, wata muhimmiyar shekara ce ta karfafa aikin yin kwaskwarima daga dukkan fannoni, kana shekara ce ta farko wajen gudanar da harkokin kasar bisa doka daga dukkan fannoni. Ana fatan za a iya ganin matakan a zo a gani da za a dauka yayin da ake gudanar da harkokin kasa bisa doka, ta yadda kowa zai iya samun daidaito da adalci yadda ya kamata.

Ban da manyan lamuran da suka shafi ci gaban kasar Sin, ana mai da hankali sosai kan batutuwan da suka shafi zaman rayuwar jama'a, kamar su yadda za a kyautata muhallin halittu, yadda za a kiyaye muradun jama'a yayin da ake yin gyare-gyare kan aikin yin rajistar iyalai da dai sauransu. Madam Zheng, wata 'yar birnin Beijing ta gaya mana cewa, ta fi dora muhimmanci kan batun kara fahimtar jama'a kan batun abincin da aka sauya wa kwayoyin halittu, wanda karon farko ne aka gabata da wannan batun cikin takardar farko da kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta fitar a wannan shekarar da muke ciki. Ta kara da cewa,

"Ban gane sosai ba kan irin wannan abinci, akwai bukatar da a kara fahimtar jama'a kan wannan batu, ta yadda za a san cewa, irin wannan abinci zai gina jiki ko lalata jiki."

Yanzu kafofin watsa labarai da ma'aikatan tarukan biyu suna shirya sosai. A kwanan nan an kaddamar da cibiyar watsa labarai ta tarukan biyu, babban manaja wannan cibiya Zhao Yudong ya furta cewa,

"Zannuwan tebur da za a yi amfani da su ba sabbi ba ne, kuma wata ka'idar da muka bi ita ce idan ana iya yin amfani da abu na da, to ba za mu sayi sabo ba. Ko da haka, amma mun mai da hankali sosai kan aikinmu na ba da hidima, har ma mun yi gwaje-gwaje sau da yawa, a kokarin samar da hidima mafi kyau a yayin tarukan biyu. "(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China