in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nazari game da yankin masana'antu da Sin ta kafa a kasar Habasha
2015-02-27 16:25:06 cri

A jihar Oromia dake kudu maso gabashin birnin Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, akwai wani yankin masana'antu da ya shahara, wanda wani kamfani mai zaman kansa ya kafa, wanda kuma ya zamo yankin masana'antu irin sa na farko a kasar.

Yanzu haka dai gwamnatin kasar Habasha ta riga ta mai da wannan yanki daya daga cikin ayyukan kasa da aka fi baiwa muhimmanci bisa shirin raya masana'antun kasar.

A kan kira kasar Habasha kololuwar tsaunukan Afrika, sai dai kasar kuma na ja da baya a fannin tattalin arziki, don haka tana bukatar jarin waje don raya bunkasuwar tattalin arzikinta.

A shekarar 2009, kamfanin Qi Yuan na lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin, ya soma zuba jari don kafa yankin masana'antu a kasar, yankin da girmansa ya kai muraba'in kilomita 5. Yanzu haka kuma an riga an kammala kashin farko bisa shirin da aka yi. Kuma masana'antun dake cikin yankin sun kai 24, cikin su akwai 15 da suka riga suka soma ayyukansu.

Wannan yankin masana'antu na gabas na kara taka muhimmiyar rawa wajen inganta hadin kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen Sin da Habasha, da kuma ci gaban tattalin arzikin wurin.

Mataimakin daraktan kwamitin kula da harkokin yankin masana'antu na gabas Mista Jiao Yongshun ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Habasha na matukar goyon bayan kafuwar wannan yanki a fannonin haraji, da kudin musanya, da zirga-zirgar jiragen ruwa, da kuma dokokin shari'a da dai sauransu. Jiao ya ce,

"Kasar Habasha kasa ce da ba ta da mashigin teku, ba ta da tasoshin jiragen ruwa, saboda haka wannan yankin masana'antu ya zama wani wurin na musayar kayayyaki. Gwamnatin kasar Habasha tana dora muhimmanci sosai kan ayyukanmu, har ma ta kaddamar da wata dokar musamman kan ayyukan yankin. Ban da wannan kuma, bayan shekaru biyu da kafa yankin, kasar ita ma a nata bangare ta kafa wani yankin masana'antu, da suke yi koyi daga fasahohinmu."

Kamfanin LiFan na kasar Sin dake yankin masana'antu na gabas shi ne kamfanin kera motoci da ya fi girma a kasar Habasha. Manajan kamfanin Mista Wang Fei, shi ne Basine daya tilo dake cikin kamfani a yankin, a yayin da yake tsokaci kan kamfanin, Wang ya ce,

"Mun soma kafa kamfaninmu a watan Mayu na shekarar 2014, mun zuba jari na dalar Amurka miliyan 4.6, girman wurin ya kai muraba'in mita 10,700. Muna dora muhimmanci kan kera motoci masu samfurorin 320, 620, 520, 530, da SUV da dai sauransu. Kamfaninmu ya kasance kamfanin harhada motoci da ya fi kyau a kasar Habasha. Yanzu akwai ma'aikata 'yan yankin 57, yawancinsu tsoffin ma'aikata ne da suka yi aiki a wurin har shekaru 3 zuwa 4, dukkansu suna da kwarewa sosai."

Mersha Ayele 'dan shekaru 29 a duniya, wanda kuma ke aiki a wannan kamfani ya gaya mana cewa,

"Kamfanin LiFan shi ne kamfanin kera motoci da ya fi girma a kasar Habasha, yana kuma kara shahara sosai a duniya. Ina aiki a nan har shekaru fiye da 5, albashin da nake dauka yana iya ciyar da dukkan iyali na. Ban da wannan kuma, kamfanin ya kan ba mu kudi kyauta. Gaskiya ni da abokan aikina muna jin dadin aiki a nan."

Kamfanin Hua Jian dake kera takalma na kunshe da ma'aikata 2800 'yan asalin wurin, da kuma ma'aikata Sinawa sama da 110. Demis, 'dan shekaru 24 da haihuwa, daya ne daga cikin jami'an kamfanin, yanzu yana iya Sinanci sosai, ana kuma kiran sa da sunan Sinanci na "Shanghai", yayin da yake hira da wakilinmu ya bayyana cewa,

"Na koyi abubuwa da yawa a nan a cikin shekaru uku, kamfanin Hua Jian ya ba ni dama mai yawa. Na taba koyon Sinanci a birnin Dongguan na kasar Sin, yanzu na kasance jami'i a wannan kamfani. Saboda kamfaninmu ya ba mu dama da yawa, hakan ya sa dole mu yi kokari sosai. Na yi imanin cewa, mu jami'ai 'yan kasar Habasha, da sauran ma'aikatan kamfaninmu dake nan Habasha, dukkanmu muna iya kokarin gudanar da ayyukanmu yadda ya kamata. Bugu da kari, za mu karfafa kwarewarmu, domin ciyar da tattalin arzikin kasarmu gaba." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China