in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen yammacin Afrika na taro domin yaki da matsalar mutanen da ba su da kasa ta asali
2015-02-26 10:48:30 cri

Wani taron ministoci ya bude a ranar Laraba a birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire domin janyo hankalin kasashen yammacin Afrika wajen yaki da matsalar mutanen da ba su da kasa ta asali, annobar da ke kamari a wannan shiyya, inda ake samun wasu mutanen da ba su da wata takardar haifuwa ko wata takardar 'dan kasa, lamarin da ke ci gaba da karuwa. Lokaci ya yi na bullo da wata mafita da kuma taimakon kasa da kasa domin baiwa kasashenmu dokoki da kayyayakin da suka dace domin kawo karshen wannan matsala, in ji shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara a yayin bikin bude taron.

A cewar babban jami'in hukumar 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR), wanda da ya shirya taron, kimanin mutane miliyan 10 da ke cikin wannan matsala suke rayuwa a duniya. A yammacin nahiyar Afrika, duk da rashin nagartattun alkaluma, ana ganin akwai irin wadannan mutane da ba su da kasa ta asali kimanin 750000.

Ya kamata mu mai da hankali wajen yaki da wannan matsala, musamman ma a matsayin matsala ta shiyyar, in ji Alassane Ouattara tare da imanin cewa, hanya guda ta rage gibin 'yan Afrika da suka rasa kasa ta assli ita ce hadin gwiwar kasa da kasa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China