150306-bikin-bazara-na-Sinawa-kashin-uku-Lubabatu.m4a
|
Bikin bazara na sabuwar shekarar Sinawa a wannan shekara aka kawo karshensa a jiya Alhamis 5 ga wata, wato ranar 15 ga wata na farko bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. Don haka, jiya ya kasance wata rana ta musamman a nan kasar Sin, wadda ake kira Yuanxiao. Yuanxiao daya ce daga cikin ranakun bukukuwan gargajiya na kasar Sin, wanda kuma da ita ce take kawo karshen dukkanin bikin bazara. Domin samun karin haske, sai a biyo mu cikin shirin.(Lubabatu)