150227-bikin-bazara-na-Sinawa-kashin-biyu-Lubabatu.m4a
|
A yanzu haka, ana murnar bikin bazara a duk fadin kasar Sin, bikin da ke alamanta shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar. Wannan sabuwar shekarar da aka shiga kuma ta kasance shekarar rago ko tunkiya, wato bisa al'adar Sinawa ta kirga shekaru da dabbobi. Domin samun karin haske a kan al'adun da suka shafi bikin bazara na Sinawa da kuma al'adar ta kirga shekaru da dabbobi, sai a biyo mu cikin shirin.