150218-Bikin-bazara-a-nan-kasar-Sin-Sanusi.m4a
|
Kasar Sin kasa ce da ke mai da hankali kan aikin gona, a shekaru aru aru da suka gabata, ana amfani da taurari domin kokarin gudanar da harkokin aikin gona kamar yadda ake fata. Sakamakon haka, aka kirkiro kalandar wata a nan kasar Sin bisa tsarin tafiye-tafiyen taurari. Bisa wannan kalandar ce, ake fara shiga sabuwar shekara a lokacin sanyi, wato a yayin da ake hutu bayan aka yi girbin amfanin gona.
Bisa al'adar galibin sassan kasar Sin, aka fara shagulgulan bikin bazara ne a ran 23 ko 24 ga watan sha biyu bisa kalandar wata. Alal misali, a ran 23 ko 24 ga watan sha biyu, galibin iyalin Sinawa su kan fara tsaftace dakunansu, wato kawar da dukkan tsoffin abubuwa marasa kyau daga gida, sannan a yi bikin girmama manzon dafa abinci.
Bugu da kari, a daren ranar 30 ga watan sha biyu, bayan an ci abinci masu dadi da dare, kusan dukkan iyali su kan yi hira suna jiran gari ya waye domin murnar isowar sabuwar shekara, wato ranar 1 ga watan farko na sabuwar shekara. Bayan gari ya waye a safiyar ranar 1 ga watan farko, matasa su kan tafi gidajen tsoffi domin nuna musu girmamawa. Wato tun daga ran 23 ga watan sha biyu zuwa ranar 15 ga farkon watan sabuwar shekara, kusan kowace rana, ana da shagulgulan murnar bikin bazara.
Sabo da kasar Sin tana da girma, ana cin abinci iri daban daban a yankuna daban daban. Galibi a arewacin kasar Sin, ana cin Jiaozi, wani irin abinci da aka yi da garin alkama, inda ke kunsa nama da kayan lambu a cikinsa. Amma a kudancin kasar Sin, ana cin shinkafa da aka dafa da 'ya'yan itatuwa. Ban da abinci na Jiaozi da shinkafa, a kan teburin iyalin Sinawa, akwai kifi, naman kaji da kayayyakin lambu iri iri, kuma kowace miya tana da ma'ana.
A baya a kan shafe kusan kwanaki 20 ana murnar wannan biki musamman a yankunan karkara. Amma ga wadanda suke aiki a kamfanoni da hukumomin gwamnati, ba su da dogon lokacin hutu, a da su kan huta na kwanaki 3 kawai, amma yanzu su kan huta na kwanaki 7, wato su fara hutu a karshen ranar watan sha biyu, amma daga rana ta bakwai ta watan farko na sabuwar shekara, dole ne su koma ofis, ko kamfanonin da suke aiki. Yanzu, a wasu yankunan karkara ma ba a huta na kwanaki 20 kamar yadda ka saba yi a da ba sakamakon bunkasuwar masana'antu a garuruwansu, sabili da haka, yanzu galibin manoma ma su kan koma wuraren aikin yi bayan rana ta 7 ko 8 ga watan farko na sabuwar shekara.
Manufar wannan biki mai muhimmanci ga Sinawa, ita ce haduwa da iyalai bayan tsawon shekara don murnar shigowar sabuwar shekara bisa kalndar gargajiyar kasar Sin inda za a ci abinci tare. (Sanusi/Ibrahim Yaya)