in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Liang Zi wadda ke daukar hotuna a nahiyar Afirka
2015-02-25 19:12:55 cri

Liang Zi, 'yar birnin Beijing ce, kuma ta shiga aikin soja tun tana yarinya, inda ta taba zama mai daukar hotuna a lokacin yaki, har ta samu lambar yabo. Tun daga shekarar 2000 ya zuwa yanzu, a cikin wadannan shekaru 15, Liang Zi ta yi tattaki zuwa wasu kasashen Afirka, ciki har da Lesotho, Saliyo, Eritrea da kuma Kamaru da dai sauransu, don gudanar da bincike kan al'adun kabilun Afirka har sau fiye da goma. Masu sauraro, yau a cikin shirin namu, za mu yi i muku bayani ne kan labarin Liang Zi.

Liang Zi tana sha'awar yawon shakatawa da kuma kundunbala. Tun tana yarniya tana da sha'awar yin nazari game da yanayi mai ni'ima da nahiyar Afirka ke da shi, da kuma al'adunsu na musamman. A lokacin, Liang Zi tana da wani buri, wato zuwa yawon shakatawa a nahiyar Afirka, domin daukar hotunan abubuwan da a baya ta ke jin labarinsu ta yadda za ta gan su a zahiri. A shekarar 2000, ta cimma wannan burin, inda ta tafi yawon shakatawa kasar Lesotho dake kudancin Afrika, duk da cewa abokanta sun gargade ta da ka da ta tafi.

"Wasu mutane sun gaya mini cewa, mutanen Afrika ba su da zumunci, kuma za su lahanta ni, ban da wannan kuma, ana samun yaduwar wasu cututtuka, ciki har da zazzabin cizon sauro. Amma, na gaya musu cewa, ina son in tafi don ganin ainihin Afrika, wannan shi ne buri na. Yayin da na iso wani karamin kauye a kasar Lesotho,na fahinci cewa, mutanen wurin suna da kirki sosai, sun karbe ni hannu bibbiyu."

Wannan yawon shakatawa da ta yi a kasar Lesotho ya canza yadda Liang Zi ta fahimci Afirka a zuciyarta. A ganinta, mutanen wurin suna da kirki da kuma kwazo, dukkansu sun karbe ta hannu bibbiyu. Liang Zi ta kuma dauki hotunan abubuwan musamman dake ba ta sha'awa da mamaki a yayin da ke zaune da kabilun nahiyar.

"Al'ummar nahiyar ce suka kirkiro kide-kide da raye-rayensu, har ma da tufafinsu na gargajiya da suke sanya wa. Kabilun da ke zaune a wadannan wurare suna da kwazo babu alamar lalaci a idonsu. Kuma muna cin abinci tare,sannan sun dauki tamkar dan uwansu. Komai ya yi kyau, tun daga lokacin,nake ganin ba zan iya daina zuwa kasashen Afirka yawon shakatawa ba, na yi tafiye-tafiye a wannan nahiyar."

Ba kamar sauran masu zuwa yawon shakatawa ba, Liang Zi ba ta je yawon shakatawa don ganin namun daji na musamman na nahiyar Afirka ba, da hasken rana da teku masu ni'ima. A madadin haka, ta kan shiga cikin kabilun da ke wurin, don ganin al'adunsu da kuma yadda suke zama. Tun da ta isa wannan nahiyar a karon farko, ta zabi wata hanya ta daban, wato ba kwana a otel ba, a maimakon haka tana zama tare da mutanen wurin.

"Na kan yi kwanaki 10 zuwa 20 a kauye, saboda kwanaki 3 zuwa biyar ba za su ishe ni ba, ina son na fahimci yadda suke zama sosai, da kuma banbancin dake tsakaninmu a fannin al'adu, da yanayin zaman rayuwarsu."

A wancan lokaci, Sinawa da suke yawon shakatawa kamar yadda Liang Zi take, wato ita kadai ta ke yawon shakatawa a kasashen Afirka, kuma yawancin Sinawa ba su san nahiyar Afirka sosai ba. A ganinsu, Afirka kamar wata kasa ce ba nahiya ba, ba su san cewa, akwai kasashe 54 a nahiyar Afirka ba, wadanda ke da harsuna da al'adu na musamman.

"A yayin da na tafi Afirka a karon farko, ban gayawa mahaifiyata ba, bayan na komo daga kasar Lesotho,sai gidan talibijin da ke garinmu ya yi hira da ni, sai lokacin ne mahaifiyata ta san cewa,na je yawon shakatawa, amma duk da haka ba ta san ina na tafi ba, har ma ta tambaye ni mene ne Lesotho. Gaskiya a wancan lokaci, Sinawa da yawa ba su san Lesotho ba, har ma wasu manema labaru da suka yi hira da ni suka yi kuskuren kiran sunan Lesotho, a yayin da suke bayar da labarai,inda suka ce Liang Zi ta komo daga kasar Soletho."

A cikin shekaru 15 da suka wuce, Liang Zi ta je yawon shakatawa a kasashen Afrika da dama, inda ta yi amfani da na'urar daukar hoto da alkalami don rubuta labarai masu tarin yawa game da nahiyar Afirka. Ban da wannan kuma ta kaddamar da litattafan da ta rubuta, ta yadda Sinawa da yawa suka soma fahimtar nahiyar. Laing Zi ta taba cewa, sanadiyar yawon shakatawan da ta je kasashen Afrika,ya sa tana kaunar nahiyar, da kuma jama'ar wurin. Sannan tana fatan Sinawa da dama za su kara fahimtar nahiyar Afirka, kuma kamar yadda ta rungumi aradu da ka,su ma za su je kasashen Afrika don ganin wannan nahiyar mai ban mamaki.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China