150216-Ana-kokarin-kafa-naurorin-shayar-da-jariri-nono-a-nan-kasar-Sin-Bilkisu.m4a
|
Ya zuwa yanzu an kafa irin wadannan dakunan shayar da jarirai nono zalla guda 534 a birane 64 na kasar Sin, cikin wannan adadi guda 115 an kafa sune a wuraren aiki, yayin da 419 aka kafa su a wuraren jama'a. A nan birnin Beijing kadai, akwai irin wadannan dakuna guda 200, wadannan kananan dakuna sun saukakawa matan da ke shayarwa yadda za su tatsa nono ga jariransu.
An kafa irin wannan dakin a harabar kamfanin HanWang da ke yankin Zhongguancun a nan birnin Beijing, ta hanyar yiwa wani dakin taro kwaskwarima. Wannan raba wannan daki ne zuwa kananan dakuna guda uku ta hanyar amfani da gilasai,a cikinsa akwai dakin shayarwa, da dakin da iyaye mata za su rika canza wa a tskanin su, da kuma dakin wanka. Yanzu iyayen da ke shayarwa suna amfani da lokacin hutu wajen tatsa nono ga jariransu a wannan wuri. Sun kuma bayyana cewa, a hawa na uku na wannan gini an tanadi akwatunan firij-firij guda biyu,don adana nonon da suka tatsa a ciki. Dukkansu sun gamsu sosai da wannan gidan shayar da jarirai nono da aka tanadar:
"Akwai kuma manyan kujeru guda hudu a gidan, baya ga na'urorin samar da wutar lantarki, wadannan sun saukaka mana yadda mu ke tatsan nono, saboda muna amfani da na'urorin lantarki ne wajen tatsar nonon. Ban da wannan kuma, akwai wurin wanka. A wasu lokuta muna iya yin musayar ra'ayoyi kan fasahohin renon yara a wurin."
"Kafin a kafa gidan shayar da jarirai nono,mu kan tatsi nono ne a ban daki, muhallin ba kyau, kuma hakan na iya shafar wasu."
Sakamakon ci gaban da aka samu game da fasahar shayar da jarirai nonon-Uwa a nan kasar Sin, iyaye mata da yawa sun zabi wannan hanyar ta shayar da jarirai. Wasu mata ko da yake su kan koma wurin aiki bayan hutun haihuwa, amma suna kokarin ganin sun shayar da jariransu nonon-Uwa zalla, inda suka zabi hanyar tatsar nono a wurin aiki, bayan haka kuma su kawo nonon gida don shayar da jariransu. Ga wadannan mata, abin da ya fi ba su wahala shi ne, rashin wani wurin da ya dace da za su rika tatsar nono a wuraren aikinsu, ko ba su iya ajiye nonon da suka tatsa yadda ya kamata. Saboda haka ana iya cewa, irin gidan shayar da jarirai mama da kamfanin HanWang ya kafa ya warware babbar matsala da suke fuskanta. Wata jami'a a kamfanin madam Xiao ta gaya mana cewa, wannan gidan mama yana da amfani kwarai. Ta ce,
"Akwai ma'aikata 500 a kamfaninmu, yawancinsu mata ne, saboda haka akwai iyaye mata masu renon yara da yawa a nan. A da, muna da wani dakin taro a hawa na hudu, na'urorin dake ciki suna da kyau, kuma yana da tsabta, inda mu ke gayyatar matan da ke shayarwa da su rika amfani da wurin wajen tatsar nono.Yayin da ita kuma babbar kungiyar kwadago ta birnin Beijing ta samar mana wasu na'urori. "
Irin gidajen shayarwa kamar wadanda aka kafa a kamfanin HanWang, wadanda suka samu goyon baya daga wajen kungiyar kwadago ta birnin Beijing sun kai 200. Tun daga farkon shekarar 2014, kungiyar kwadago ta birnin Beijing ta shawarci kamfani da manyan kungiyoyi na birnin da su kafa gidaje na musamman don saukakawa ma'aikatai mata wajen da za su rika tatsar nono don shayar da jariransa, ta kuma dauki alkawarin samar da na'urori masu tsafta ga wadannan kamfani da kungiyoyin. Suna fatan a cikin shekaru 3 masu zuwa za a kafa irin wadannan gidajen shayarwa guda 1000 a birnin Beijing
Amma, idan aka yi la'akari da yawan mutanen dake birnin Beijing, ko da an kafa gidajen shayarwa guda 1000 ba za su iya biyan bukatun mata masu shayarwa ba. Ban da kafa gidajen shayar da jarirai nona-zalla a wuraren aiki, akwai bukatar gaggawa warware yadda ake shayar da jarirai nono a wuraren jama'a. Ga yadda wasu iyayen da ke shayarwa ke cewa:
"Ba abu ne mai sauki ba, idan ina son fita waje, dole ne in fita a cikin sa'o'i uku."
"Gaskiya ba abu ne mai sauki ba, na kan shayar da jariri na a cikin mota ne"
Shugabar sashen kula da harkokin ba da hidima kan kiwon lafiyar mata da yara na hukumar kiwon lafiyar kasar Sin, madam Zhang Shikun ta ce, kasar Sin na fatan karfafa ganin an kafa gidajen shayar da jarirai nono. Madam Zhang ta bayyana cewa,
"Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta gabatar da wata shawarar '10m² of Love', wato wani wuri dake da muraba'in mita 10 don saukakawa mata wajen shayar da jarirainsu. Muna fatan dukkan kamfanoni da kungiyoyi za su kafa irin wadannan na'urori ga mata masu renon yara."
Yanzu, babu wata dokar dake shafar kafa gidajen shayar da jarirai nono a nan kasar Sin, hakan ya kasance wani muhimmin dalili da ya sa babu isassun irin wadannan na'urorin a wuraren jama'a. Bisa wannan yanayin da ake ciki, shehun malami a jami'ar Tsinhua ta kasar Sin Zheng Luze ya gabatar da shawara cewa,
"A ganina, ya kamata a gaggauta kafa wani tsari na zaman al'umma, ga misali, kada a yi la'akari da ko wani kamfani ya kafa gidan shayar da jarirai nono ga ma'aikatansa mata, ko a'a a yayin da ake kimanta ko zai iya tsallake shadurradan da aka dora masa. Hakan zai taimakawa wajen gudanar da irin wannan aikin ga al'umma yadda ya kamata." (Bilkisu)