in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron Davos na shekarar 2015
2015-02-11 17:24:45 cri

Daga ranar 21 zuwa 24 ga watan Janairun shekarar 2015 ne aka gudanar da taron dandalin tattalin arziki na duniya na wannan shekara a birnin Davos na kasar Switzerland, taron da ya saba hallara shugabannin kasashen duniya, shugabannin 'yan kasuwa da masana'antu, kungiyoyin kare hakkin bil-adama, masana, kafofin watsa labarai da sauransu.

Baya ga batun tattalin arziki an kuma tattauna wasu muhimman batutuwa kamar rashin daidaito, matsalar canjin yanayi da ci gaba mai dorewa da dai sauransu a wannan karon.

Bugu da kari taron na bana, ya kuma duba manyan batutuwa guda uku da ke damun duniya a halin yanzu, wato barazanar kungiyar da ke da'awar kafa daular musulunci ta IS, rikicin Rasha da Ukraine, da kuma faduwar farashin mai a kasuwannin duniya.

A jawabin musamman da ya gabatar firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana cewa, taron Davos na da muhimmanci sosai ga tattalin arzikin duniya. Kana tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da karuwa cikin yanayi mai kyau, duk da wasu canje-canje da tattalin arzikin kasar Sin da na kasashen ketare ke fuskanta. A nan gaba, kasar Sin za ta ci gaba da gudanar da harkokin kudi yadda ya kamata, domin tabbatar da bunkasuwar aikin cikin yanayi mai kyau da karko, kana, tsarin tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da samun kyautatuwa a halin yanzu.

Sai dai masana na ganin cewa, duk da ci gaban masana'antun da aka samu, har yanzu akwai matasa da dama da ke fama da matsalar rashin aikin yi, don haka suka ce wajibi ne a magance wannan matsala muddin a na bukatar kawar da manyan abubuwan da ke sanya irin wadannan matasa shiga ayyukan ta'addanci sakamokon rashin aikin yi.

Bugu da kari, wajibi ne a magance manyan matsalolin da mahalarta taron na bana suka tabo ta yadda dandalin zai amsa sunansa na zama madubin tallata albarkatu, hajojin kasashe da kamfanoni don jan hankalin masu sha'awar zuba jari. Matakin da a karshe zai kai ga bunkasa tattalin arzikin duniya baki daya. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China