Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ne ya bayyana hakan yau Jumma'a yayin taron manema labarai.
Mr. Hong ya ce, Dalai Lama dan siyasa ne da ke gudun hijira, wanda ya ke fakewa da batun addini domin kawo baraka ga kasar Sin.
A jiya ne shugaba Obama na Amurka ya marabci Dalai Lama a wata addu'ar liyafar karya kumullo a birnin washington,ko da ya ke wasu rahotanni na cewa,bai gana da shi kai tsaye ba.(Ibrahim)