150121-Tasirin-gangamin-da-aka-shirya-a-Faransa-kan-yakin-da-taaddaci-Sanusi.m4a
|
Wadannan jami'ai daga kasashen duniya da shugaban kasar Faransa François Hollande sun yi jerin gwano tare da 'yan kasar Faransa don nuna kiyayya ga ayyukan ta'addanci. Hakazalika kuma, an yi zanga-zanga a sauran birane da yankunan kasar a wannan rana. Rahotanni na cewa, mutanen da suka halarci zanga-zangar a wannan rana ya kai fiye da miliyan daya.
Mahukuntan kasar Faransa sun ce, an yi zanga-zangar ce don girmama mutanen 17 da suka mutu a kasar a sakamakon harin da 'yan ta'adda suka kai a mujallar nan ta barkwanci da wani shagon sayar da kayayyaki na zamani.
Sai dai kafin harin na Faransa, an kai munanan hare-hare masu alaka da ta'addanci a kasashen Sin, Pakistan, Somaliya, Najeriya da sauran sassan dabam-dabam na duniya, inda aka halaka rayukan jama'a baya ga dukiyoyin da suka salwanta.
Masana na ganin cewa, ba wai irin gangamin da aka shirya a kasar Faransa ne zai magance matsalar ta'addanci da ta kasance ruwan dare gama duniya ba. Kamata ya yi kasashen duniya su hada kai don kawo karshen wannan matsala.
Bugu da kari, akwai bukatar a warware manyan matsalolin da ke haddasa kai irin wadannan hare-hare tun daga tushe bisa la'akari da abubuwan da suka shafi addini, al'ada, yanayin zaman takewar al'umma da sauran muhimman batutuwa. (Ibrahim/Sanusi Chen)