141223-zaman-lafiya-ya-fi-zaman-arziki-bako.m4a
|
Kwanan baya, yayin da wakilinmu Bako ke zantawa da wani dan kasuwar kasar Nijeriya Halifa Adamu da ke kasuwanci a birnin Guangzhou, ya bayyana cewa, "zaman lafiya ya fi zaman arziki", duk da yake, zamansa a kasar Sin ba ya kawo masa arziki sosai ba, amma ya samu zaman lafiya, kuma yana fatan dangantakar Sin da Nijeriya za ta ci gaba da samun kyautatuwa, har ma zai iya kawo duk iyalinsa zuwa Sin.(Bako)