in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gidan rediyon CRI da jaridar People's Daily sun zabi muhimman abubuwa 10 da suka faru a shekarar 2014
2015-01-01 15:46:03 cri

A yau ne, gidan rediyon kasar Sin, wato CRI da jaridar People's Daily suka zabi wasu muhimman al'amura 10 da suka faru a shekarar 2014.

Wadannan abubuwa 10 sun hada da, taron APEC da aka shirya a nan Beijing, manufar tafiyar da harkokin diplomasiyya ta kasar Sin tsakanin manyan kasashen duniya ta samu ci gaba sosai. Halin rashin ci gaban tattalin arzikin kasashen duniya bai samu kyautatuwa kamar yadda ya kamata ba, amma saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ya taimakawa sauran kasashen duniya. Yadda kasashen yammacin Afirka suke fama da cutar Ebola, kasar Sin ta ba da taimako kamar yadda dan uwa ke yi ba tare da son kai ba. Bacewar jirgin sama samfurin MH307 na kamfanin zirga-zirgar jirgin saman Malaysia, da har yanzu ba a same shi ba ko da yake kasashe da dama sun shiga aikin gano wannan jirgi. Rikicin Ukraine ya kara tsananta halin dake tsakanin kasashen Amurka da EU da kasar Rasha. Matakin sanya takunkumi kan kasar Rasha da kasashen Amurka da EU suka dauka da matakin mayar da martin na kasar Rasha sun kara kawo hadari ga tattalin arzikin kasashen duniya. Kungiyar IS ta kaddmar da hare-hare a yankin Gabas ta tsakiya, kawancen da sojan kasa da kasa ke yi kan wannan kungiya bai kai ga samun sakamako kamar yadda ake fata ba. Kasar Japan ta yi watsi da manufar tsaron kasa, sauran kasashen Asiya dake makwabtaka da ita sun bayyana abubuwan da ke jawo hankulansu. Matsalar da ta kunno kai a unguwar Furgeson ta tayar da hankali a duk fadin kasar Amurka, amma har yanzu ba ana amfani da dokokin nuna bambancin launi fata a kasar Amurka. Dan Adam ya samu ci gaba sosai a binciken saurarin sama sakamakon saukar da na'urar Philae ta yi a tauraron Comet bayan ya yi shekaru 10 yana bin sawun tauraron. Kasashen Amurka da Cuba sun shirya dawo da dangantakar diplomasiyya da ke tsakaninsu. Sabo da haka, an kawo karshen cacar bakin da ke tsakanin sassan biyu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China