141223-bataliyar-sin-sudan-ta-kudu-saminu
|
A jiya Litinin ne rukunin farko na bataliyar sojojin kiyaye zaman lafiya ta kasar Sin, wadda za ta tashi zuwa kasar Sudan ta Kudu ta kammala shiri, tare da bikin rantsuwa a birnin Laiyang dake lardin Shandong na nan kasar Sin.
Wannan dai bataliya za ta isa kasar Sudan ta Kudu ne domin gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya a Juba, babban birnin kasar, bisa umurnin MDD. Haka kuma, wannan ne karo na farko da kasar Sin za ta kafa bataliyar sojojin kiyaye zaman lafiya, domin gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD a ketare.
A yayin bikin rantsuwar da aka gudanar a jiya Litinin, mataimakin babban kwamandan yankin sojan na Jinan na kasar Sin Liu Shenyang, ya tabbatar da umurnin fara ayyukan kiyaye zaman lafiyar da rukunin farko, na bataliyar sojojin kiyaye zaman lafiyar za ta aiwatar a kasar Sudan ta Kudun.
"Bisa umurnin kwamitin tsakiya mai kula da harkokin sojan kasa ta Sin, za a aike da bataliyar sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa kasar Sudan ta Kudu ne, domin gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya na MDD. Ana kuma fatan za a iya karfafa ayyukan jagorancin sojin namu cikin sauri kamar yadda ya dace, domin tabbatar da cimma nasarar wannan aiki."
A watan Yuli na shekarar nan ne MDD ta bukaci kasar Sin, da ta kafa wata bataliyar sojojin kasa ta kiyaye zaman lafiya a hukunce, matakin da ya sanya kwamitin tsakiya mai kula da harkokin sojan kasar ta Sin, ba da umurni ga yankin sojan Jinan, da ta kafa wannan bataliya.
Haka kuma, Liu Shenyang ya ce, runkunin farko na wannan bataliya za ta tashi zuwa Sudan ta Kudu nan da 'yan kwanaki, lamarin da ya nuna cewa matsayin kasar Sin na ci gaba da dagama a harkokin kiyaye zaman lafiyar kasa da kasa.
"Bataliyar sojojin kasa da kasar ta Sin da za ta yi ayyuka a ketare, na da muhimmin tasiri a harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya. Ana sa ran sojojin kiyaye zaman lafiyar na Sin a Sudan ta Kudu za su mai da hankali kwarai wajen gudanar da ayyukansu, don gane da yanayin da kasar ke ciki a halin yanzu, kana za su yi aiki da makamai mafiya inganci, kuma dukkanin dakarun tawagar na da kwarewa a wannan aiki."
Tun dai lokacin da aka fara tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa Sudan ta Kudu a shekarar 2005, bisa jimilla an tura sojoji 8036 daga yankin sojan Jinan, domin gudanar da wannan aiki. Kwamandan bataliyar sojojin kiyaye zaman lafiyar Wang Zhen ya ce, tun kaddamar da wannan bataliya, an horas da dakarun yanayin kasar Sudan ta Kudu, da kuma wasu kalubalolin da za su iya fuskanta a kasar.
Sakamakon horaswar da suka samu, a halin yanzu daukacin sojojin suna da kwarin gwiwar gudanar da ayyukansu na kiyaye zaman lafiya a Sudan ta Kudu cikin nasara. Ya ce,
"bisa ka'idojin sojojin kasa na MDD, tabaliyar ta tsara wani daftarin gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya, da ya hada da a ba da jagoranci cikin aikin kiyaye zaman lafiya, da yake-yake, da tsara ayyukan soji, da kuma tabbatar da gudanar da ayyukansu cikin nasara, a dukkanin fannoni da dai sauransu. Kaza lika, an yi atisaya da dama bisa dukkanin fannonin, inda aka cimma nasarar gudanarwar atisaye guda 8, da suka shafi kiyaye tsaron rundunar bataliya, da na sintiri a birane da sauran yankuna."
Bugu da kari a farkon watan Disambar bana, MDD ta kaddamar da ayyukan bataliyar bisa binciken da ta yi. Tawagar musamman ta MDD dake kunshe da masu bincike 6 sun amince da kwarewar sojojin bataliyar, game da aikin kiyaye zaman lafiya, suna ganin cewa, sojoji sun shirya caf domin gudanar da wannan aiki, sun kuma dauki makamai masu inganci na shirinsu kafin tashi zuwa kasar Sudan ta Kudu.
Ban da wannan kuma, an kafa wani ajin dakaru mai kunshe da sojoji mata guda 13 cikin wannan bataliya, domin gudanar da wasu ayyukan musamman. Kuma wannan shi ne karo na farko da sojoji mata na kasar Sin, za su halarci aikin kiyaye zaman lafiya na MDD. Shugabar wannan bangare Wang Pei ta bayyana wa manema labarai cewa,
"manyan ayyukammu daidai suke da na sojoji maza, amma akwai wasu ayyuka na musamman gare mu, kamar taimakawa mata da yara, kan bukatunsu na musamman, a lokacin da sojojin suke gudanar da aikin sintiri, da bincike kan mata a tashohin binkice, da kula da harkokin mata da yara, a fannin taimakon jin kai, da kuma ba da taimako ga mata da yaran game da shawarwarin inganta tunani idan har akwai bukata."
Bisa shirin da aka tsara, da farko sojoji 180 na bataliyar za su tashi zuwa kasar ta Sudan ta Kudu, ta jigaren sama dauke da kayayyakin da ake bukata na yau da kullum a farkon watan Janairu dake tafe, kafin daga bisani wasu karin sojojin su isa kasar ta jiragen sama ko na ruwa. (Maryam)