Kwanan baya, yayin da wakilinmu Bako ke zantawa da wani dan kasuwa matashin kasar Nijeriya Abubakar da ke harkokin kasuwanci a kasar Sin, ya bayyana cewa, ya kamata matasan Nijeriya da su bar zauna gida banza, sun yi karatu, sannan sun zo kasar waje, alal misali kamar Sin, don kara yaukaka dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Nijeriya.