141224-Shekaru-15-da-dawowar-yankin-Macau-hannun-kasar-Sin-Sanusi
|
Bisa tsarin kasar Sin, gwamnatin tsakiya ce ke nada wanda zai jagoranci irin wadannan yankuna na musamman bisa amincewar kwamitin zabe.
Yankin musamman na Macau ya koma hannun kasar Sin ne ranar 20 ga watan Disamba na shekara ta 1999, bayan an cimma wata yarjejeniyar tsakanin Sin da bangaren turawan Portugal dake mulkin yankin a ranar 1 ga watan Disamba na shekara ta 1887 da ake kira "yarjejeniyar Peking".
A karkashin tsarin kasa daya tsarin mulki biyu da ake aiwatarwa, yankin na Macau ne ke da iko a harkokin da suka shafi takardar kudi, tsarin kwastan, harkokin shigi da fici, 'yan sanda, kula da kan iyakoki da kuma harkar shari'a. Yayin da gwamnatin tsakiya ke da iko a kan harkar tsaro na yankin da kuma harkokin da suka shafi kasashen waje da sauran muhimman fannoni.
Harkar yawon shakatawa na samar wa GDP na yankin kashi 50 cikin 100, yayin da bangaren samun kudaden shigar yankin ke samun kashi 70 cikin 100 daga harkar yawon shakatawa.
A wannan karon an shirya shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyara yankin Macau daga ranar 19 zuwa 20 ga wannan Disamba na shekarar 2014 don halartar bikin cika shekaru 15 da komawar yankin zuwa hannun kasar Sin da kuma rantsuwar kama aiki na gwamnatin yankin karo na 4. Wannan ne karo na farko da shugaba Xi Jinping ya kai ziyara yankin Macau tun bayan da ya hau kujerar shugabancin kasar ta Sin.
Tun lokacin da yankin musamman na Macau ya dawo hannun kasar Sin, gwamnatin kasar Sin ta bullo da tsarin bayar da ilimi kyauta tun daga matakan makarantun reno, firamare da kuma sakandare. Baya ga yadda gwamnatin Sin ta inganta harkokin kiwon lafiya, sufuri da sauran muhimman sassan more rayuwar al'ummomin dake yankin. (Ibrahim, Sanusi Chen)