in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimmancin tunawa da ranar kisan kiyashin Nanjing na shekarar 1937
2014-12-18 16:39:25 cri

A ranar Asabar 13 ga watan Disamban shekarar 2014 ne a karon farko kasar Sin ta shirya bikin tunawa da kisan kiyashin da sojojin kasar Japan suka yi wa Sinawa a birnin Nanjing a shekarar 1937.

Bikin wanda ya samu halartar shugaba Xi Jinping da manyan jagororin jam'iyyar kwaminis mai mulkin kasar, ya gudana ne a babban dakin taro na tunawa da kisan kiyashin dake birnin Nanjing, hedkwatar lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin.

A ranar 13 ga watan Disambar shekarar 1937 ne dakarun sojojin kasar Japan suka mamaye birnin na Nanjing, wanda a wancan lokaci ke matsayin helkwatar kasar Sin, inda suka kwashe kwanaki 40 suna yi wa Sinawa kisan kare dangi.

An yi kiyasin cewa cikin wadannan kwanaki, sojojin na Japan sun yiwa sojoji Sinawa da fararen hula da suka mika wuya su sama da 300,000 yankan rago, baya ga sauran fararen hula da suka hallaka, suka kuma yiwa mata kusan 20,000 fyade.

A watan Fabrairun shekara ta 2014 ne majalissar wakilan jama'ar kasar Sin ta sanya ranar 13 ga watan Disamban kowace shekara, ta zamo ranar tunawa da wannan lamari, domin nunawa duniya irin ta'asar da dakarun kasar ta Japan suka aikata.

Masu fashin baki na fatan kebe wannan rana da kasar Sin ta yi zai zamo wani muhimmin mataki na bayyana munin abin da ya auku a wancan lokaci, tare da bayyana matsayin kasar Sin game da kin jinin amfani da karfin tuwo da burin ganin an kare darajar bil'adama da kuma tabbatar da zaman lafiya da lumana a daukacin fadin duniya. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China