141205-abincin-halal-na-kasar-Sin-1-lubabatu.m4a
|
Musulunci ya yadu har zuwa nan kasar Sin a karni na bakwai, don haka, kasar Sin ta kasance tana da dimbin musulmi, wadanda yawansu ya kai sama da miliyan 20, musamman ma wasu kabilu 10 mabiya addinin, ciki har da Hui da Uygur. Abincin halal na musulmin kasar Sin suna da yawa da nau'o'insu suka kai sama da 5000, wadanda suka hada al'adu na musulmi, da ma na Sinawa a gu daya. Sai a bi mu cikin shirin a tattaunawar da muka yi da Fatimah Jibril bisa ziyarar da ta kai wasu sassan musulmi na kasar Sin, musamman domin samun fahimtar nau'o'in abincin halal na musulmin kasar Sin da ma al'adun da ke jibantar abincin.