141201-jirgin-ruwan-tsaron-teku-na-da-amfani-bako.m4a
|
A makon da ya gabata, kasar Sin ta mika wani babban jirgin ruwan tsaron teku ga gwamnatin Nigeriya. Yayin da wakilinmu Bako ke zantawa da mataimakin hafsa-hafsoshi a fannin ruwa na Nijeriya, Bala, ya bayyana cewa, Jirgin da kamfanin kera jiragen ruwa na CSIC wato China Shipbuilding Industry Corporation, an mika shi ne ga kasar Nigeriya a birnin Qidong, dake lardin Jiangsu na gabashim kasar Sin. Jirgin mai tsawon mita 95.5 da fadin mita 12.2 yana iya fitar da ruwa da ya kai tan 1,800, abinda ya sa zai zama mafi girma kuma mai dauke da kayan zamani cikin jiragen ruwan tsaron teku da Nigeriya ke da su a yanzu,in ji kamfanin na CSIC, kuma jirgin na da amfani sosai ga gwamnatin Nijeriya.(Bako)