in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hidimomin halal za su karu a shekaru masu zuwa
2014-12-08 10:05:14 cri

Wani rahoto da aka fitar na nuna cewa, akwai yiyuwar masana'antun da ke samar da kayayyaki da hidimomin da suka shafi harkokin halal za su kara karuwa cikin shekaru masu zuwa.

Rahoton wanda cibiyar bunkasa tattalin arzikin Islama da gwamnatin Dubai tare da tallafin Dinar standard suka fitar ya nuna cewa, yadda ake samun karuwar harkokin tattalin arziki na Islama, kamar bankin Islama da abincin halal ko kayayyakin da suka dace da addinin Islama, sun saukaka rayuwar musulman da ke tafiye-tafiye a sassa daban-daban na duniya.

Shugaban cibiyar Abdullah Al Awar ya ce, yanzu haka kasashen Sin da Italiya su ne a kan gaba wajen samar da kayayyaki irin su dankwali da gyale da mata musulmi ke amfani da su, baya ga abincin halal da kusan ake samu a dakunan cin abinci na manyan biranen kasar Sin.

Rahoton ya kuma nuna cewa, yanzu haka ana samun karuwar musulmai daga kasashen Larabawa da kudu maso gabashin Asiya da ke kai ziyara kasashe na Sin da Italiya, yayin da kasar Australia ta kasance a kan gaba wajen samar da nama na halal a yankin Asiya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China