in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kokarin shugabannin duniya na magance matsalar sauyin yanayi
2014-12-14 15:37:14 cri

A ranar Talata 2 ga watan Disamban shekarar 2014 ne aka bude taron masu ruwa da tsaki kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo na 20, kuma taron wadanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar Kyoto karo na 10 a birnin Lima hedkwatar kasar Peru.

Babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon ya sha tunatar da al'ummar duniya cewa, kowa da kowa a duniya yana dandana tasirin sauyin yanayi, kamar ambaliyar ruwa, mahaukaciyar guguwa, kwararowar Hamada, fari, zaizayar kasa da sauran bala'u inda rayukan jama'a da dukiyoyi ke salwanta.

Manazarta na cewa, taron na wannan karo ya kasance wani muhimmin bangare cikin shawarwarin dake gudana tsakanin bangarori daban-daban kan batun sauyin yanayi, wanda kuma zai kawo babban alfanu ga auna yiwuwar cimma sabuwar yarjejeniyar yanayi a shekarar 2015 a birnin Paris.

Sai dai a lokacin da ake musayar ra'ayoyi kan yadda za a magance wannan matsala, kananan kasashe na ci gaba da zargin kasashen da suka ci gaba da rashin cika alkawuransu game da sauyin yanayi.

A baya kasar Jamus ta yi alkawarin zuba jari na dala biliyan 1 ga asusun kiyaye muhalli a shekaru hudu masu zuwa, yayin da Sin a matsayinta na kasa mai tasowa ta sanar da yin kokari tare da kasashen duniya wajen tunkarar matsalar sauyin yanayi tare da ninka gudummawar da ta bayar.

Muhimmin batu da za a tattauna a wannan karo shi ne, matakan da ya dace a dauka wajen tinkarar sauyin yanayi wato na farko, kara tabbatar da matakan da kasashen duniya za su dauka wajen tinkarar sauyin yanayin kafin shekarar 2020 da tattaunawa ayyuka, da matakan da kasahen duniya za su dauka bayan shekarar 2020, domin inganta karfin tinkarar kalubale na sauyin yanayi.

Masu fashin baki na ganin cewa, idan har ba a magance matsalar sauyin yanayi dake barazana ga ci gaban duniya ba, hakika wannan matsala za ta yi mummunan tasiri ga ci gaban tattalin arziki, lafiya, zamantakewar jama'a da sauran fannoni na rayuwa har ma da ci gaban duniya baki daya. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China