141203-Ranar-Nakasassu-ta-duniya-Sanusi.m4a
|
A irin wannan rana a kowace shekara, a kan shirya taruka da laccoci da shirye-shirye a kafofin watsa labarai inda ake gabatar da jawabi game da nasarori da matsaloli da wannan rukuni na jama'a ke fuskanta. A wasu lokutan kuma ana tattaunawa da shugabannin Nakasassun don jin ta bakinsu game da tallafin da suke samu daga gwamnatoci ko kungiyoyi masu zaman kansu na gida da na waje da kuma irin kalubalen da suke fuskanta.
Bugu da kari, wata dama ce ta shigar da Nakasassun cikin harkokin tattalin arziki, Ilimi, siyasa da sauran bangarori na rayuwa kamar sauran jama'a masu lafiya, ta yadda za su bayar da gudummawa ga ci gaban al'umma.
Sai dai duk da irin wadannan tanade-tanade da aka yi wa Nakasassun da nufin inganta rayuwarsu, su ma gwamnatoci a matakai daban-daban na bullo da shirye-shirye da za su taimakawa Nakasassun daina yin barace-barace a kan tituna.
Masu fashin baki na cewa, akwai bukatar a kara tallafin da ake baiwa Nakasassun ta yadda za su kasance masu dogara da kansu tare da ba da gudummawa ga ci gaban kasa maimakon zama mabarata a kowane lokaci. (Ibrahim/Sanusi Chen)