in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gudummawar da farfesa Graham Furniss ya bayar ga adabin Hausa
2014-11-30 16:07:24 cri

A ranar Laraba 19 ga watan Nuwamban shekarar 2014 ne sananne a fannin nazarin harshe da adabin Hausan wato farfesa Graham Furniss kana tsohon direktan makarantar nazarin harsunan yankin gabashi da nahiyar Afirka ta jami'ar London ya kawo ziyara sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin CRI da ke nan birnin Beijing a lokacin da ya zo nan kasar Sin.

Farfesa Furniss ya samu digirinsa na farko a ilmin harshen Hausa da hayayyar dan Adam a jami'ar London a shekarar 1972, kuma ya samu digiri na uku a jami'ar London a shekarar 1977. Farfesa Furniss sananne ne a duniya a fannin nazarin adabin hausa. Ya kuma wallafa litattafai da makaloli da suka shafi harshen Hausa da dama, baya ga litattafan da suka shafi wannan fanni da ya duba. A shekarar 2009, an zabe shi mamban cibiyar nazarin harshen Hausa a Burtaniya, kana an ba shi lambar yabo ta OBE a shekarar 2013 sakamakon gudummawar da ya bayar a aikin bunkasa harshen Hausa.

Ya ce, duk da ci gaban kimiyya da aka samu har yanzu harshen Hausa na bunkasa ganin yadda matasa ke ci gaba da yin rubuce-rubuce a harshen Hausa, inda ya ba da misali da matasa masu shirya wasan kwaikwayo na zamani da litattafan soyayya da makamantansu. Sai dai ya bukaci malaman jami'o'i da suka kware a harshen Hausa da su yi harshen gata ta hanyar duba irin wadannan litattafai da matasa ke rubuta don gyara irin kura-kuran da ke ciki, hakan zai karfafa musu gwiwar ci gaba da ba da tasu gudummawar ga ci gaban harshen na Hausa.

Farfesa Furniss ya kuma yaba da irin rawar da kafofin watsa labarai ke takawa wajen fassara sabbin kalmomin kimiya da suka bigiro ta yadda za su muhalli a cikin harshen.

Duk da cewa, farfesa Furniss ya yi ritaya daga aikin koyarwa amma ya ce, zai ci gaba da yin mu'amala da sauran abokansa da ke sassan daban-daban a duniya don ci gaba da ba da gudummawa ga ci gaban harshen Hausa. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China