141119-Kudurorin-da-taron-G20-karo-na-9-ya-cimma-a-Australia-Sanusi.m4a
|
Yayin taron shugabannin kungiyar G20 sun sha alwashin aiki tare don yaki da cutar Ebola, cutar da yanzu haka ke shafar sassan tattalin arziki, baya ga kasancewar ta babbar barazana ga harkokin kiwon lafiyar duniya. Bugu da kari shugabannin kungiyar sun yi kira ga bankin duniya da asusun bada lamuni na IMF, da su ci gaba da tallafawa kasashen dake fama da wannan cuta.
An kuma bukaci bada kulawa ga harkar bincike, da samar da sahihan magunguna, da alluran rigakafi, da kayan aikin magance cutar ta Ebola Ebola da kula da lafiyar ma'aikatan lafiya da ke aikin yaki da cutar.
Har ila shugabannin sun kuduri aniyara bunkasuwar tattalin arzikin duniya, da kyautata zaman rayuwar jama'a, da kuma samar da guraban ayyukan yi a matsayin muhimman ayyuka da kungiyar ta sanya gaba.
Sanarwar da mahalarta taron suka bayar a karshen ganawar tasu ta kuma bayyana cewa, koda yake wasu daga muhimman kasashe masu saurin ci gaba a fannin tattalin arziki sun riga sun bunkasa, a yanzu haka kuma tattalin arzikin duniya na farfadowa sannu a hankali, duk da rashin daidaito da ake samu tsakanin yankuna daban daban a fannin bunkasuwar tattalin arziki.
Har wa yau sanarwar ta ce kawo yanzu ba a kai ga biyan bukatun al'ummar duniya wajen samar da aikin yi ba, kana akwai hadari da kasuwar hada-hadar kudade ke fuskanta, da ma batun matsalolin siyasa tsakanin kasashe daban daban, da dai sauran batutuwa.
Bugu da kari sanarwar ta bayyana alkawarin da shugabannin kasashe membobin kungiyar ta G20 suka yi, na kara yin hadin gwiwa tsakaninsu don sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arziki da tsara shirin kara yawan GDP na dukkan kasashe membobinta da kashi 2 cikin dari nan da shekaru biyar masu zuwa.
Sanarwar ta kara da cewa, shugabannin sun dauki matakai da dama, don tabbatar da adalci kan tsarin biyan haraji, da kara sa ido kan aikin biyan harajin, da yaki da laifin zambar biyan haraji. Baya ga amincewa da wani shirin yaki da cin hanci da rashawa., batun sauyin yanayi da sauran fannoni
Masu fashin baki na ganin cewa, idan har aka samu nasara aiwatar da wadannan batutuwa hakika za a samu babban ci gaba a fannoni da dama a duniya. (Ibrahim/Sanusi Chen)