141114-ciniki-ta-hanyar-internet-1-lubabatu.m4a
|
Kamfanonin kasar Sin masu hada-hadar cinikayyar ta yanar gizo sun kafa sabon tarihi, inda Alibaba, kamfanin sayar da kaya ta yanar gizo mafi girma a duniya ya sayar da kayan da kimar su ta haura kudin kasar RMB miliyan dubu 36, kimanin dalar Amurka miliyan dubu 5 da miliyan dari 9 ke nan cikin awa 13 da rabi kawai da aka fara bikin sayayya ta yanar gizo a ranar 11 ga wata.
Yanzu haka, ciniki da ake yi ta hanyar internet na kara zama ruwan dare a nan kasar Sin da ma wasu sassan duniya, sai a bi mu cikin shirin, mu leka me harkar ke kawo wa zaman rayuwar dan Adam a zamanin yanzu.