A cikin makon da ya wuce, shugabanni da wakilai na membobin kungiyar ta APEC 21, da shugabannin sassan masana'antu, da shahararrun masana a yankin Asiya da tekun Pasifik kimanin 1500 suka hallara a nan birnin Beijing, inda suka cimma matsaya a fannoni da dama, kamarsu kaddamar da yunkurin kafa yankin cinikayya cikin mai 'yanci a yankin Asiya da tekun Pasifik, da sa kaimi ga yin mu'amala da juna, da neman samun bunkasuwa ta hanyar samar da sabbin kayayyaki da sauransu, tare da zartas da tsarin Beijing da sanarwar dangantakar abokantaka a yankin Asiya da tekun Pasifik, wadanda suka kara tabbatar da hanyar da za a bi, da makasudi, da kuma matakai da za a dauka wajen hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki a wannan yanki.
Membobin kungiyar ta APEC sun samar da rabin yawan GDP na duniya, da jimillar cinikayya kashi 44 cikin dari a duniya. Da haka ana iya ganin cewa, taron kungiyar APEC da aka yi a birnin Beijing a wannan karo na da muhimmanci kwarai da gaske. Bayan shekaru 13, Sin ta sake jagoranta taron kungiyar APEC. A cikin makon da ya wuce kuma, an cimma matsaya kan batutuwa sama da dari daya a gun taron.
A cikin sakamakon da aka samu, abin da ya fi jawo hankali shi ne kaddamar da yunkurin kafa yankin cinikayya mai 'yanci, da sa kaimi ga tabbatar da taswirar yankin cinikayya mai 'yanci a yankin Asiya da tekun Pasifik. Wannan ya nuna cewa, an sami babban ci gaba wajen kawar da gibin cinikayya tsakanin shiyya shiyya. Dangane da haka mMinistan masana'antu na Sin Gao Hucheng ya bayyana cewa,
"Wannan taswira ta tabbatar da tsari da hanyar da kungiyar APEC za ta bi wajen sa kaimi ga kafa yankin cinikayya cikin mai 'yanci. Hakan zai kasance sakamako mai matukar ma'ana da aka samu a tarihin kungiyar APEC."
A yayin taron, Sin ta sanar da kebe kudi dala biliyan 40 wajen kafa asusun hanyar siliki, domin taimakawa da zuba jari ga kasashen dake dab da yanki, da hanyar siliki, wajen kafa manyan kayayyaki masu amfanin jama'a, da yin hadin gwiwa da sauransu.
Wannan ra'ayi ya samu amincewa da babban yabo daga sauran membobin kungiyar ta APEC. Shugaban Bangladesh Abdul Hamid ya furta cewa,
"Tsahon lokaci mun share fagen hada hanyar hanyoyin mota, da hanyar jirgin kasalayin dogo namu, da na kasashe makwabtanmu. Kuma muna shirya kafa wani filin jirgin sama na duniya a yankin tsakiyar kasar, ta yadda kasarmu za ta kasance muhimmiyar mahada ta jiragen sama a yankin Asiya da tekun Pasifik."
Ban da haka, a kokarin samun karin karfin bunkasa tattalin arziki, da samun karin ci gaba mai dorewa, bangarori daban daban sun yi shawarwari kan hadin gwiwa a fannonin sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin yanar gizo, da fitar da albarkatun teku da sauransu, tare da cimma matsaya da dama. Shugaban Darektan hukumar sashin harkokin duniya kasa da kasa ta ma'aikatar masana'antu ta Sin, Zhang Shaogang ya bayyana cewa,
"Ya zuwa shekarar 2018, za a kokarta kammala aikin kafa linzamin darajar kungiyar APEC, da dakin ajiye alkaluman karuwar cinikayyawata ajiyar alkaluma wadda za ta bayyana darajar kayayyakin kungiyar APEC da yawan karuwar ciniki. Kuma an amince da kafa cibiyar tashar jirgin ruwa ta musamman a birnin Shanghai, wadda za ta taka muhimmiyar rawa wajen yin mu'amala da juna. Kuma an dauki birnin Tianjing a matsayin wurin samar da ganyaye masu inganci. Za kuma a kaddamar da wannan aiki a karshen shekarar nan ko farkon shekara mai zuwa."
Dadin dadawa, wannan taro ya kafa wani dandalin gudanar da ayyuka tsakanin kasashe daban daban, musamma ma ga shugabannin Sin da Japan, wadanda suka gana da juna bayan shekaru da dama.
A ranar 10 ga wata, shugaban Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na Japan Abe Shinzo a babban dakin taruwar jama'a. Wanda kuma wannan ne karo na farko da shugabannin kasashen biyu suka gana da juna, cikin shekaru biyu da rabi. Game da wannan batu, shugaban cibiyar nazari kan harkokin duniya kasa da kasa ta Sin, Qu Xing ya bayyana cewa,
"Kasashen biyu za su kyautata dangantaka tsakaninsu a kai a kai. Wanda hakan ya dogaro kan matsayar Japan game da shawarwarrin da kasashen biyu suka cimma a fannoni hudu."(fatima)