Wata sanarwar da kungiyar AU ta bayar ta ce, kwamishinan kula a harkokin zaman lafiya da tsaro na kungiyar AU Smail Chergui da manzon musamman na babban sakataren MDD mai kula da yankin Great Lakes Said Djinnit sun gana a ranar Lahadi a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha kan wannan batu.
Sanarwar ta ce, ganawar ta ba su damar nazarin yadda za a aiwatar da yarjejeniyar da kuma manufar kokarin da ake na tabbatar da zaman lafiya,tsaro,kwanciyar hankali da ci gaba a yankunan na Great Lakes.
Bugu da kari, tattaunawar ta mayar da hankali kan shirye-shiryen taro na gaba da aka shirya gudanarwa a watan Janairun shekarar 2015 a Addis Ababa, yayin taron kolin kungiyar ta AU.(Ibrahim)