141105-Manufar-Sin-na-samar-da-ilimi-kyauta-ga-kananan-kabilun-kasar-Sanusi.m4a
|
Wannan manufa ta baiwa daliban kabilu daban-daban da ke karatu a makarantar midil a yankin jihar Xinjiang fiye da dubu 90 damar shiga makarantar sakandare ba tare da biyan sisin kobo ba.
Shi dai wannan yanki da ke kudu da tsaunukan Tianshan da ake kira da suna yankin Xinjiang ta kudu ya hada da Kashgar,Hotan,Kizilsu,Kirghiz da kuma Aksu.
Sannan yanki ne da kabilun Uygur,Kirgiz,Mongolia da Tajik da sauran kananan kabilu ke zaune. Bayanai sun nuna cewa,rashin ci gaban tattalin arziki da harkokin sadarwa na daga cikin abubuwan da suka sa yankin ya ke fuskantar koma bayan ilimi.
Bugu da kari, a wannan shekara gwamnati kasar Sin ta baiwa kowa ne dalibin makarantar sakandare kudin dukkan zangon karatunsa,yayin da su kuma dalibai daga kauyuka marasa sukuni daga irin wadannan yankuna aka ba su kudaden sayan litattafai na tsawon shekaru uku na zangon karatu da kudaden dakin kwana da sauransu.
Wannan manufa na gwamnatin Sin a cewar masu fashin baki, za ta baiwa daliban kananan kalibu da marasa karfi damar samun Ilimi mai inganci kamar kowanne dan kasa cikin saukin tare da cike gibin da ke akwai tsakanin 'ya'yan masu hali da marasa hali ta fuskar samun Ilimi a kasar ta Sin mafi yawan al'umma a duniya.
A cewar masu sharhi,wannan mataki ya tabbatar da kudurin shugabannin kasar Sin na inganta rayuwar al'ummomin kasar daga dukkan fannoni.(Ibrahim/Sanusi Chen)