141029-Matakin-da-kasar-Sin-ta-dauka-na-gudanar-da-harkokin-mulkin-kasa-bisa-doka-Sanusi.m4a
|
Wannan shi ne cikakken zaman taro na farko da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta dauki batun tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka a matsayin taken taron.
Kudurin ya zayyana matsalolin da kasar Sin ke fuskanta a fannin tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka, da gabatar da burin da za a cimma da kuma ka'idojin da za a bi a wannan fanni. Sa'an nan ya gabatar da wasu sabbin ra'ayoyi da matakan tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka.
Bugu da kari ya amsa wasu tambayoyi game da dangantakar dake tsakanin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta Sin da aikin tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka. Haka zakila ya gabatar da wasu shirye-shirye a fannonin kafa dokoki, gudanar da ayyuka bisa doka, yin shari'a cikin adalci, sanya jama'a su bi dokoki da dai sauransu, wanda ya amsa kiran da jama'ar kasar suka yi da kulawar da suke nunawa. Wannan zai kara kafafa yunkurin da ake na tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka.
Masana na ganin cewa, yayin da kasar Sin ke zurfafa gyare-gyare ya zama wajibi ta kara inganta rawar da dokoki ke takawa, domin wannan wani babban ci gaba ne da Sin ta samu a fannin tsara dokokinta. (Ibrahim/Sanusi Chen)