141022-Matakan-da-kasashen-duniya-suke-dauka-kan-Ebola-Sanusi.m4a
|
Yanzu haka cutar Ebola ta halaka mutane sama da 4,000 tun bayan da cutar ta bullo a kasashen yammacin Afirka da suka hada da Liberia, Guinea, Saliyo da kuma wasu kalilan a Najeriya baya ga wasu sama da dubu 8 da suka kamu da cutar. Wannan ya sa wasu kasashen da ke makwabtaka da wadannan kasashe da ke fama da wannan cuta daukar wasu matakai da suka hada da rufe kan iyakokinsu, dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa kasashen ko daukar fasinjojin da suka fito daga wadannan kasashe.
Baya ga kasashen yammacin Afirka da ke fama da wannan cuta, yanzu haka an samu rahoton mutuwar masu dauke da cutar a kasashe kamar Amurka, Jamus da wasu kasashen Turai. Wannan ya sa kasashe irin su Amurka da Burtaniya daukar matakan binciken zafin jikin fasinjojin da suka shigo kasar ta jiragen sama daga kasashen da ke fama da wannan cuta don hana yaduwar cutar a cikin kasashen su.
Hukumar lafiya ta duniya WHO da wasu kasashe, ciki har da kasar Sin sun aike da taimakon kayayyakin kiwon lafiya da tawagar ma'aikatan lafiya zuwa kasashen da suke fama da wannan cuta.
Har yanzu cutar Ebola mai saurin kisa ba ta da magani, don haka ma'aikatan lafiya ke kira ga jama'a da su kara daukar matakan kariya daga kamuwa da cutar, yayin da gwamnatocin kasashen da ke fama da cutar ke kara fadakar da jama'a tare da ware makuden kudade don tunkarar wannan cuta da yanzu haka ta kasance mafi hadari a duniya. (Ibrahim/Sanusi Chen)