141015-Matakan-kasar-Sin-na-kawar-da-talauci-a-cikin-alumma-Sanusi.m4a
|
An bayyana talauci a matsayin wani yanayi na rashin muhimman kayayyakin more rayuwa kamar abinci, ruwan sha mai tsafta, tufafi, wurin zama, muhalli mai kyau, Ilimi, kayayyakin kiwon lafiya da sauransu.
Daya daga cikin muhimman manufofin kungiyoyin kasa da kasa irin su bankin duniya da MDD shi ne kawar da talauci a tsakanin al'umma.
A shekara ta 2008, bankin duniya ya yi kiyasin cewa, akwai mutane biliyan 1.29 da ke zama cikin talauci, kuma wannan matsala ce da ta shafi dukkan sassan duniya, ciki har da kasashen da ke da karfin tattalin arziki.
Shi ma asusun tallafawa yara na MDD (UNICEF) ya yi hasashen cewa, rabin yara na duniya ko yara biliyan 1.1 a duniya na zama cikin talauci.
Bisa ma'aunin kasar Sin kasancewarta kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, akwai matalauta 82 a kasar a shekara ta 2013. Sannan a cikin shekaru fiye da 30 da suka gabata, mutane fiye da miliyan 600 sun rabu da talauci a kasar.
Yanzu haka mahukuntan kasar Sin sun bayyana kudurinsu na rage adadin da ya kai miliyan 10 na matalauta a kauyukan kasar a bana tare da bullo da tsarin kawar da talauci, tsarin intanet da hanyoyin kawar da talauci daban daban.
Masana sun bayyana cewa, wasu daga cikin abubuwan da ke haddasa matsalar talauci sun hada da yadda shugabanni ke amfani da mukamansu ta hanyar da ba ta dace ba, matsalar tsaro, batun da ya shafi jinsi, matsalar canjin yanayi, da rashin kungiyoyin al'ummomi da ba su da bakin fada a ji da dai sauransu.
Muddin ana bukatar kawar da wannan matsala a cikin al'umma, wajibi ne a inganta aikin gona, lafiya, Ilimi tare da kawar da shingayen da ke kawo tafiyar hawainiya ga ayyukan gwamnati, sannan a samar da shirye shiryen inganta rayuwar al'umma da kara samar musu da kafofin samun kudaden shiga. (Ibrahim/Sanusi Chen)