Bikin baje-koli na Africast wanda hukumar kula da shirye-shiryen talabijin da rediyo na Najeriya wato NBC ta dauki nauyin shiryawa, na gudana ne a otel din Sheraton dake birnin Abuja, inda aka samu halartar manyan kafofin watsa labarai na Najeriya da na duniya, kamar su gidan talabijin na NTA, gidan rediyon muryar Najeriya wato VON, kamfanin dillancin labarai na Najeriya wato NAN, gami da gidan rediyon muryar Amurka wato VOA, da gidan rediyon Faransa da sauransu. Shahararren kamfanin watsa shirye-shiryen talabijin na kasar Sin dake Najeriya wato StarTimes shi ma ya halarci bikin.