141021-zan-yi-kokari-don-daga-matsayin-diploasiyya-dake-tsakanin-Bako.m4a
|
A ranar 15 ga wata, sabon jakadan da ke kasar Sin Mustapha Inoussa ya mika takardun kasa ga shugaban kasar Sin Xi Jinping a hukunce, inda ya bayyana wa mai girma shugaban Xi kyakkyawar gaisuwa da takwaransa na jamhuriyar Nijer mai girma Muhamadou Issoufou ya bayar da farko, sannan nan ya fada masa tarihin karatunsa a kasar Sin a shekarun 26 da suka gabata. Jakadan Mustapha ya ce, duk da cewa, a cikin shekaru 26 da suka gabata, bai samu damar sake komawa kasar Sin ba, amma kullum ya kan duba littattafai da shafin Internet don kara sanin halin da ake ciki a wannan babbar kasar, yanzu, kamar masu iya magana kan cewa, "Gani ya kore ji", ya sake dawowa kasar Sin a matsayin jakadan kasarsa zuwa kasar Sin, zai yi iyakacin kokarinsa don daga matsayin diplomasiyya da ke tsakanin wadannan kasashe, sabo da huldar dake tsakanin wadannan kasashe idan da ba ta zama tta farko ba, za ta zama ta biyu a cikin manufar diplomasiyya na jamhuriyar Nijer.(Bako)