in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF ya rage hasashen ci gaban duniya da ya yi a baya
2014-10-08 15:10:36 cri

Asusun ba da lamuni na duniya wato IMF ya bayar da wani sabon rahoto kan hasashen ci gaban tattalin arzikin duniya a jiya Talata 7 ga wata, inda ya rage hasashen karuwar tattalin arzikin duniya na bana da na badi da ya taba yi a baya, tare da cewar dalilin da ya sa ya rage wannan hasashe shi ne tabarbarewar tattalin arzikin yankunan kasashen Turai masu amfani da kudin EURO da kuma raguwar saurin karuwar tattalin arziki da wasu kasashe masu saurin bunkasuwa ke yi. Ban da wannan kuma, IMF ya nuna damuwa ga gaza samun farfadowar tattalin arzikin duniya yadda ya kamata da kuma rashin samun daidaito a wannan fanni.

Bisa sabon rahoton da Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya bayar kan hasashen ci gaban tattalin arzikin duniya a kwanan baya, an ce, jimillar karuwar tattalin arzikin duniya za ta kai kashi 3.3 cikin kashi dari a bana da kuma kashi 3.8 cikin kashi dari a badi, wadanda suka rage kashi 0.1 da kashi 0.2 cikin kashi dari bisa na karon da ya gabata, wato hasashen da Asusun ya yi a watan Yuni da ya gabata. Wannan kuwa ya zama karo na uku da IMF ya rage hasashen ci gaban duniya da ya yi a wannan shekarar da muke ciki.

Babban masanin ilmin tattalin arziki Olivier Blanchard yana ganin cewa, tabarbarewar tattalin arzikin yankunan kasashen Turai masu amfani da kudin EURO da kuma raguwar saurin karuwar tattalin arziki da wasu kasashe masu saurin bunkasuwa ke yi sun zama muhimman dalilan da suka haddasa raguwar wannan hasashe. Yana mai cewa,

"ko kadan ba a iya samun alamun farfadowar tattalin arzikin yankunan kasashen Turai masu amfani da kudin EURO, wanda ya ba da tasiri sosai ga farfadowar tattalin arzikin duk duniya ba."

Amma an gano haske a cikin duhu, wato rahoton ya yi kyakkyawan hasashe kan tattalin arzikin kasashen Amurka da Sin. Bisa rahoton da aka bayar, an ce, hasashen da IMF ya yi kan karuwar tattalin arzikin kasar Amurka a bana ya karu da kashi 0.5 cikin kashi dari bisa na karon ya gabata, wato jimillar karuwar tattalin arzikinta za ta kai kashi 2.2 cikin kashi dari. Sa'an nan Asusun bai canja hasashen da ya yi kan karuwar tattalin azikin kasar Sin ba, jimillar za ta kai kashi 7.4 da kashi 7.1 cikin kashi dari a bana da badi.

A ganin IMF, wannan ya sheda farfadowar tattalin arziki na tafiyar hawainiya, kana ba a samu daidaito a wannan fanni ba. Don haka, Olivier Blanchard ya yi kira ga kasashe masu ci gaba da su magance ficewa daga tsarin kudi mai sassauci tun da wuri, da kuma kara zuba jari kan muhimman ayyukan more rayuwa. Ya kara da cewa,

"ko a kasashen da ke cin basusuka, zuba jari kan muhimman ayyukan more rayuwa zai iya daidai tsarin tattalin arziki da kuma kara yawan bukatun cikin gida cikin gajeren lokaci. Ban da wannan, zai iya ba da tabbaci ga ci gaban kasa cikin dogon lokaci, yayin da ba za a kara yawan kason basusuka da ke cikin kudaden da aka samu ba daga aikin kawo albarka cikin gida."

Bugu da kari, ya kamata kasashe masu saurin bunkasuwa su sa kaimi ga aikin gyare-gyare kan tsarin tattalin arzikinsu bisa halin da suke ciki. wani abu mai muhimmanci shi ne ya kamata su shirya sosai don tinkarar komawar kudaden kasashe daban daban zuwa kasar Amurka bayan da ta aiwatar da tsarin kudi yadda ya kamata sakamakon farfadowar tattalin arzikinta. Olivier Blanchard ya bayyana cewa,

"yawancin kasashe masu ci gaba da masu saurin bunkasuwa na tinkarar wani kalubale, wato fahimtar gyare-gyaren da ya kamata su yi a wannan zamani, da kuma gyare-gyaren da kila za a aiwatar a nan gaba."

Haka zakila, rahoton ya jaddada cewa, ya kamata gwamnatocin kasashe daban daban su sake karfafa zukatansu wajen tsara shiri don daidaita matsalolin da aka samu sakamakon tabartarewar tattalin arzikin duniya da kuma kalubalolin da za a samu sakamakon raguwar saurin bunkasuwa da ake hasashe.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China