141003-koyon-sinanci-na-samun-karbuwa-a-duniya-lubabatu.m4a
|
Taron da aka gudanar a karshen watan Agustan da ya wuce dangane da aikin gudanar da jarrabawar harshen Sinanci a kasashen ketare ya nuna cewa, ya zuwa watan Maris na shekarar 2014, yawan mutanen da ke koyon harshen Sinanci a duk fadin duniya ya zarce miliyan 100, lamarin da ya shaida cewa, harshen Sinanci na a sahun gaba a cikin harsunan duniya da aka fi sha'awar koyo. Domin samun karin haske kan harkar koyon Sinanci, sai a biyo mu a tattaunawar da Lubabatu da Maman Ada suka yi dangane da harkar koyon Sinanci.